Bam Ya Tashi Da Kasurgumin Dan Bindigar Zamfara, Dogo Gudali, Ya Mutu
- A karshe dai hatsabibin shugaban yan bindiga da ya dade yana addabar jihohin arewa, Dogo Gudali ya bakunci lahira
- Gudali da wasu mayakansa ya mutu ne sakamakon tashin bam da wasu takwarorinsa yan ta’adda suka dasa
- Yan ta’addan dai sun dana bam din ne da nufin murkushe dakarun Operation Hadarin Daji amma sai ya tashi kafin lokaci
Zamfara - Rahotanni sun kawo cewa kasurgumin shugaban yan bindiga da ya addabi al'ummar jihar Zamfara, Dogo Gudali, ya mutu.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Gudali ya hadu da ajalinsa ne sakamakon tashin bam da wasu mambobin kungiyarsa na ta'addanci suka dana.
Mayakan sun dana bam din da nufin kashe sojoji amma ya fada kan Dogo Gudali da mayakansa
An tattaro cewa yan ta'addan sun dana bam din ne domin kawar da dakarun rundunar soji na Operation Hadarin Daji, wadanda ke aikin kakkaba a dajin Gando da ke karamar hukumar Bukkuyum ta jihar.
Zargin Batanci: Gwamnatin Sokoto Ta Bayyana Irin Matakin Da Za Ta Dauka Kan Masu Batanci Ga Annabi (SAW)
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zagazola Makama ya rahoto wata majiya ta sojoji na cewa:
"An dana bam din ne domin sojoji, amma sai ya tashi kafin lokaci sannan ya kashe shugaban yan bindigar mai hatsari, Dogo Gudali da wasu mayakansa.
"Dogo Gudali da tawagarsa san dade suna addabar Anka, Gummi, Bukkuyum da wasu yankuna na jihohin Sokoto da Kebbi."
Jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin kasar na daya daga cikin jihohin da ke fama da hare-haren yan bindiga wanda ya ki ci ya ki cinyewa.
Yan daba sun taso wasu garuruwan Kano a gaba, al'ummar yankunan na zaman dar-dar
A wani labari na daban, mun kawo a baya cewa al'ummar garuruwan karamar hukumar Dala ta jihar Kano sun shiga yanayi na tashin hankali saboda yawan hare-hare da wasu yan daba ke kai masu.
Kamar yadda dan majalisa mai wakiltan al'umomin a majalisar dokokin jihar, Lawan Hussaini Dala (NNPP) ya bayyana, bata garin na shigowa yankin tun ido na ganin ido sannan su farmaki al'umma.
Bayan nan sai su yi masu fashin kayayyakinsu da kuma kone-kone tare da sukar mutane da wuka. Dan majalisar ya kuma ce a cikin irin haka ne wasu mutane suka rasa rayukansu sannan wasu sun fara barin gidajensu.
Asali: Legit.ng