“Na Caje Shi Fiye Da Kima”: Jami’in Sojin Ruwa Ya Mari Tinubu Yayin da Yake Direban Tasi a Amurka

“Na Caje Shi Fiye Da Kima”: Jami’in Sojin Ruwa Ya Mari Tinubu Yayin da Yake Direban Tasi a Amurka

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya ba da labarin wani abu da ya faru a lokacin da yake aiki a matsayin direban tasi a kasar Amurka
  • Tinubu ya bayyana a cikin littafin rayuwarsa cewa wani sojan ruwa ya taba marinsa saboda ya caje shi kudi fiye da kima a lokacin da ya dauke shi a tasi dinsa
  • Shugaban Najeriya ya kuma bayyana yadda ya tallafawa kansa a matsayin direban tasi kafin ya fara karatu a Chicago

Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana cewa wani jami'in rundunar sojin ruwa ya taba marinsa kan ya caje shi kudi da yawa ba tare da ya sani ba lokacin da yake aikin tuka tasi a kasar Amurka.

An bayyana hakan ne yayin da yake ba da tarihin yadda ya fara a cikin wani littafin tarihin rayuwarsa wanda jaridar Daily Sun ta wallafa a ranar Asabar, 24 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Shugaba Tinubu Ya Faɗi Gaskiyar Yadda Ya Cire Tallafin Man Fetur Ranar Rantsarwa

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
“Na Caje Shi Fiye Da Kima”: Jami’in Sojin Ruwa Ya Mari Tinubu Yayin da Yake Direban Tasi a Amurka Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kwararren dan jarida Mike Awoyinfa ne ya rubuta tarihin rayuwar tasa mai taken, "Tinubu: Rayuwata a matsayin direban tasi a Amurka".

Abun da na fuskanta a matsayin dalibi a Amurka, Tinubu ya bayyana

A cikin labarin, Tinubu ya ce ya yi aiki a matsayin direban tasi mara lasisi a Chicago, kasar Amurka yana daukar fasinjoji daga filin jirgin sama zuwa wuraren da za su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kasar ya ce ya yi aikin tukin ne domin daukar dawainiyar kansa kafin ya je makaranta.

Ya ba da labari:

"Mun samu wata mota mara rijista, wanda muke amfani da ita a matsayin tasi. Muna aiki a filin jirgin sama inda muke daukar fasinjoji, sannan ba ko'ina ba, kamar su otel saboda an haramtawa direbobin tasi marasa lasisi aikata haka.
"Mun aikata haka na dan lokaci don hada wasu kudade. Bolaji ya tafi Tennessee, yayin da ni na tunkari Chicago.

Kara karanta wannan

Tsohon Minista Ya Yabi Tinubu a Kan Irin Nade-Naden Mukaman da Yake Yi a Mulki

"Ya kamata da na fara makaranta a watan Afrilu. Na jinkirta har zuwa Satumba domin na samu wasu kudade. Ina zuwa Chicago, kai tsaye na tafi kwalejin Richard Daley. Ya kasance mai ban sha'awa sosai.
"Na yi nasarar biyan kudin gidana da na makarantar jami'ar jihar Chicago. Na kara da ayyuka iri-iri kamar maigadi da tsaron wuri."

Na caji jami'in sojin ruwa fiye da kima bisa kuskure - Tinubu

Da yake ci gaba da magana kan lamarin, ya ce wani jami'in sojin ruwa da ya dauka ya amsa masa da mari a fuska saboda ya caje shi fiye da kima, kasancewar wurin da zai je bai da nisa.

Tinubu ya ce:

"A matsayin direban tasi, wani abu da ba zan taba mantawa da shi ba shine lokacin da na caje wani jami'in sohin ruwa da ke dawowa kasar kudi da yawa. Ba da gangan bane.
"A zahiri, ban san hanyar ba. Babu GPRS a zamanin da zai kai ka inda za ka. Saboda haka ya bani kwatancen gidansa a yankin Virginia.

Kara karanta wannan

Neja: Bene Ya Ruguje Tare Da Kashe Yaro Dan Shekara 15, Gwamnati Ta So Rushe Benen Kafin Yanzu

"Na fada masa farashin sai mutumin ya amsa da bani mari a fuskana. Ya ce ya kamata na san ainahin farashin da ake caja zuwa wajen da ya ambata. Ya mareni sannan ya bani kudin."

Badakalar takardar karatun Tinubu: Omokri ya bayyana abun da bincikensa ya nuna masa

A wani labarin, Reno Omokri, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya bayyana a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni cewa karya ne ace shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai halarci jami'ar jihar Chicago da ke kasar Amurka ba.

Da yake wallafa a shafinsa na Twitter, magoyin bayan jam'iyyar ta Peoples Democratic Party (PDP) ya ce binciken da ya gudanar nasa na kansa ya nuna cewa da gaske shugaban kasa Tinubu ya halarci jami'ar ta Amurka, kuma yana daya daga cikin manyan tsoffin dalibansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng