Ba’a Dawo Da Mohammed Dauda a Matsayin Shugaban Hukumar Leken Asiri Ba – NIA
- Hukumar NIA ta yi martani a kan rahoton dawo da mbasada Mohammed Dauda a matsayin darakta janar na hukumar leken asiri ta kasa
- Hukumar leken asirin ta bayyana labarin a matsayin kanzon kurege da yaudarar da jama'a
- Ta ce tun farko Dauda bai taba zama shugabanta ba illa rikon kwarya da ya taba yi kafin dakatar da shi
Abuja - Hukumar leken asiri ta kasa ta yi watsi da wani rahoton yanar gizo na cewa kotun daukaka kara ta dawo da Ambasada Mohammed Dauda a matsayin darakta janar na hukumar.
A cikin wata sanarwa da ya gabatarwa manema labarai a Abuja, shugaban sashin shari'a na NIA, Mista A. Wakili, ya bayyana rahoton a matsayin yaudara, rahoton Daily Trust.
Wakili ya ce
“An ja hankalinmu zuwa ga wani kagaggen labari na karya da yaudara da ke yawo a soshiyal midiya dangane da dawo da Dauda a matsayin darakta Janar na hukumar NIA da kotun daukaka kara, reshen Abuja ta yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Yana da matukar muhimmanci mu fayyace cewa Dauda bai taba zama ainahin darakta janar na hukumar ba.
“Kawai ya yi aiki ne na wucin gadi, bayan wa’adin shugabancin Ambasada Ayo Oke da dan rikon kwarya a takaice da Ambasada Arab Yadam, ya yi har zuwa lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Ambasada Ahmed Abubakar a matsayin ainahin darakta janar na hukumar.”
“Batun daukaka karar da aka yanke masa hukunci yana da alaka ne kawai da al’amuran da suka shafi korar da aka yi masa.
"Har yanzu shari'ar da ta shafi keta tsari tana nan ana jira a yanke hukunci."
Ya yi zargin cewa Dauda da mukarrabansa ne suka kitsa labarin karyar da yaudara domin batar da jama’a.
Sai dai kuma, Wakili ya ce ana jiran nazarin ainahin kwafin hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke domin sanin mataki na gaba, rahoton Daily Nigerian.
Kotu Ta Maido Shugaban Leken Asiri da Buhari Ya Kora Daga Aiki a Shekarar 2018
A baya mun ji cewa kotun daukaka kara mai zama a garin Abuja, ya maida Mohammed Dauda a kan kujerar Darekta Janar na hukumar NIA a Najeriya.
Rahoton Tribune ya ce Alkalin babban kotun na birnin tarayya ya ci tarar gwamnati, ya bukaci a biya Amb. Mohammed Dauda Naira miliyan 1.
Asali: Legit.ng