An Cafke Saurayi Da Budurwarsa Kan Sayar Da Jinjirin Da Suka Haifa A Edo
- Jami'an hukumar da ke yaƙi da fataucin ɗan adam ta cafke wani saurayi da budurwarsa bisa laifin siyar da jaririnsu
- Ana tuhumar saurayin mai suna Anthony, da budurwarsa Joy da laifin siyar da jariri ɗan wata ɗaya kan kuɗi N1.7m
- Hukumar ta kuma zargesu da ta'ammuli da miyagun ƙwayoyi, wanda shine ummul aba'isin aikata ɗanyan aikin da suka yi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Benin City, jihar Edo - Jami'in hukumar da ke yaƙi da fataucin bil'adama ta jihar Edo, sun cafke wani mai suna Anthony Igbinogun dan shekaru 48, tare da budurwarsa Joy Umukoro, ‘yar kimanin shekara 28.
An kama saurayin da budurwar tasa ne bisa laifin sayar da jaririnsu ɗan wata ɗaya domin samun kuɗin shan ƙwayoyi, kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.
Haka nan kuma, jami'an sun kama waɗanda ake tuhumar tare da wata abokiyarsu mai suna Precious James, yar kimanin shekaru 26, da ta taimaka wajen haɗasu da wanda ya sayi jaririn, a Fatakwal ta jihar Ribas.
Cire Tallafin Man Fetur: FG Ta Fara Raba 'Solar' Kyauta A Fadin Ƙasar Don Rage Raɗaɗin Da Jama'a Ke Ciki
A kan kudi N1.7m ne mutanen biyu suka sayar da jaririn
A zantawarta da 'yan jarida a Benin babban birnin jihar Edo, shugabar sashin bincike na hukumar yaƙi da fataucin dan adam ta jihar Edo, Abigail Ihonre, ta ce an sayar da jaririn a kan kuɗi naira miliyan 1.7.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta kuma ƙara da cewa jami'ansu na ci gaba da gudanar da bincike don ceto jaririn ɗan wata ɗaya, tare da cafko mutumin da ya saye shi.
A cewar Ihonre:
“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa, Joy Umukoro, ta haifi jaririn ne a watan Afrilun 2023, sai suka haɗa baki ita da saurayinta don su sayar da jaririn nasu kan naira miliyan 1.7. Ta kuma amsa laifin sayar da jaririn da ake tuhumarta da shi.”
“Ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin domin kamo waɗanda suka sayi jaririn domin a gurfanar da su a gaban kotu daga nan zuwa ranar Litinin 26 ga watan Yuni, 2023, saboda ya zamto cewa duk wanda ke da hannu a ciki ya fuskanci fushin doka kan laifukan da ya aikata.”
Yanzu-Yanzu: An Tabbatar Da Rasuwar Duka Mutane 5 Dake Cikin Jirgin Ruwan Titan Da Ya Bace A Tekun Atlantika
Saurayin da budurwar sun bayyana dalilinsu na siyar da jaririn na su
Waɗanda ake zargin sun ce sun aikata wannan ɗanyen aikin ne saboda ba za su iya kula da jaririn ba.
Sai dai jami'ar hukumar yaƙi da fataucin mutanen ta musanta iƙirarin da suka yi.
Ta ce suna ta'ammuli da miyagun kwayoyi ne, wanda hakan ya sa ba za a su iya ɗaukar dawainiyar jaririn ba, inda ta ce ganin haka ne ya sa suka yanke shawarar sayar da shi.
Jami'ar ta ƙara da cewa wannan matakin da suka ɗauka babban kuskure ne da zai iya lalata musu rayuwarsu.
Jaridar Independent ta ruwaito Abigail na cewa duk wanda ba zai iya ɗaukar ɗawainiyar ɗan da ya haifa ba, ya kawo musu shi ofishinsu maimakon siyar da shi.
Wani matashi yana neman wacce za ta haifar masa yaro kan naira miliyan 20
Legit.ng a baya ta kawo muku labarin wani matashi ɗan Najeriya da ya ke neman wacce za ta ɗauki ciki, sannan ta haifa masa yaro akan kuɗi naira miliyan 20.
Labarin wanda aka ɗora a kafar sada zumunta ya yaɗu sosai gami da janyo muhawara.
Asali: Legit.ng