Bikin Babban Sallah: Gwamnatin Kano Ta Amince Da Ba Dalibai Hutun Mako Guda
- Gwamnan jihar Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta sanar da ranakun hutu ga dalibai domin bikin babban sallah
- Ma'aikatar ilimi na jihar Kano ta ba dalibai hutun mako guda daga ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni zuwa Asabar, 1 ga watan Yuni domin bukukuwan sallah
- Wannan hutu zai shafi daukacin dalibai na makarantun kwana da na jeka ka dawo
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kano - Ma'aikatar ilimi na jihar Kano ta amince da Juna'a, 23 ga watan Yuni, a matsayin ranar fara hutun bikin babban sallah ga dukkanin makarantun jeka ka dawo da na kwana a jihar.
Bikin babban sallan wanda zai shafe tsawon mako guda zai kare a ranar Asabar, 1 ga watan Yuni.
Saboda haka, ana sa ran daukacin daliban makarantun za su dawo makaranta a ranar Lahadi, 2 ga watan Yuni yayin da masu jeka ka dawo za su koma a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni, Nigerian Tribune ta rahoto.
An bukaci iyaye su kwashi yaransu a safiyar Juma'a don tafiya hutu
Sakataren din-din-din na ma'aikatar ilimi na jihar, Malam Ahmad Tijjani Abdullahi, ya bukaci iyaye da su tabbatar da komawar yaransu makaranta a ranakun da aka sa za a dawo.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan labarai da wayar da kan jama'a na ma'aikatar ilimi a jihar Kanom Alhaji Aliyu Yusuf, kuma aka gabatar ga manema labarai a Kano a ranar Alhamis, gwamnatin jihar ta yi kira ga iyaye a jihar da su kwashe yaransu zuwa gida a safiyar Juma'a.
Malam Abdullahi ya kuma bukaci iyaye da su tabbatar da bayar da hadin kai kan ranakun da aka amince dalibai za su dawo.
Ya kuma yi masu barka da bakukuwan sallah da za yi sannan ya roke su da su zamo masu amfani ga iyayensu da kuma guje ma yawo mara amfani a lokacin hutun sallah.
Sakataren din-din din ya kuma yi gargadin cewa za a dauki matakin da ya dace kan daliban da suka saba, rahoton PM News.
An ba Abba Gida-Gida awanni 72 ya daina rusau a Kano
A wani labari na daban, an ba gwamnan jihar Kano, Abba Yusuf, wa'adin awanni 72 ya dakatar da aikin rusau da ke gudana a jihar sannan ya kira wadanda abun ya ritsa da su domin tattaunawa da nufin samun mafita.
Wata kungiyar masu rajin tabbatar da dimokradiyya karkashin inuwar Good Governance and Change Initiative (GGCI) ce ta bayar da wa'adin.
Asali: Legit.ng