“Hajiya Ki Bari Talakawa Su Sarara”: Matashiya Ta Je Kazuwa, Ta Kaso N180k Kan Kayan Abinci

“Hajiya Ki Bari Talakawa Su Sarara”: Matashiya Ta Je Kazuwa, Ta Kaso N180k Kan Kayan Abinci

  • Wata matashiya yar Najeriya ta je kasuwa don siyayyan kayayyakin bukata na gida kuma bidiyo ya nuno abubuwan da ta siya
  • A bidiyon, ta fada ma mabiyanta na TikTok cewa ta je kasuwa da N180,000 don siyan kayan abinci iri-iri
  • A karshe, ta baje kolin kayayyakin da kudinta ya iya siya mata, kuma mutane da dama sun garzaya sashin sharhi don tofa nasu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani bidiyo da ya yadu ya nuno wata yar Najeriya wacce ta je kasuwa don siyayyan kayan abinci da sauran kayan ciye-ciye na gida.

Mai amfani da TikTok, Mabel ta ce ta je sabon kasuwan, Artisan Enugu inda ta siya kayayyakin da za ta bukata na gida.

Matashiya da kayan abinci
“Hajiya Ki Bari Talakawa Su Sarara”: Matashiya Ta Je Kazuwa, Ta Kaso N180k Kan Kayan Abinci Hoto: @iam_mabel4.
Asali: TikTok

Da ta isa kasuwan tare da kanwarta, sai ta faka motarta sannan ta ziyarci sashi daban-daban na kasuwar domin samun kayayyakin abinci da na amfani.

Kara karanta wannan

An Bude Iyakar Legas Domin Shigo da Motoci, Gwamnati Ta Yi Watsi da Tsohon Tsari

Matashiya wacce ta je siyayya ta ba mutane mamaki da yawan kayyakin da ta siya

Wasu daga cikin kayayyakin da ta siya sun hada da kwai, danyen tumatir, tumatirin gwangwani, sabulun wanki, barkono, danyen nama da abubuwa da dama.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bidiyon ya nuna cewa matar ta siya kayayyakin da yawa ne, hakan na nufin za ta shafe tsawon lokaci kafin ta sake ziyartan kasuwan.

Da ta baje kolin dukka abubuwan da ta da kudin, wasu mabiyanta sun sha mamaki.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@MIRABEL ya ce:

"Ki bar talaka ya sarara, kada ki shake mu."

@Ada Aro-okeigbo ta yi martani:

"Da kin fada mana farashin abubuwan da kika siya."

@Zinny’s beauty ta ce:

"Hajiya wannan 180k naki baya karewa ne?"

@oluwabunmikolawol ya ce:

"Baaba rayuwa akwai matsayi daban-daban. Wasu 20k ne kadai ke binsu zuwa kasuwa kuma wasu basu da shi, Allah ya albarkace mu dukka.

Kara karanta wannan

Maganin barna: Uwa ta cije, ta hana danta jakar makaranta, ta mika masa buhun siminti

@Veracruz ta ce:

"Kudin Najeriya bai da kai. Mijina ya bani 100k na siyan kayan amfanin gida sannan ya nemi na kawo chanji gida."

Biloniya na neman mai kula da karnukansa, zai biya albashi miliyan N8 duk wata

A wani labari na daban, iyalan wani hamshakin mai kudi a kasar Amurka da ke zama a Landan suna neman mai raino da zai dunga kula da karnukansu guda biyu.

Wanda ya yi nasarar samun aikin zai kwashi albashi na zunzurutun kudi har naira miliyan 96.1 a shekara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng