Dalilin Da Yasa Shugaban Sojin Ruwa Mai Barin Gado Bai Mika Mulki Ga Magajinsa Ba
- Hedkwatar rundunar sojin ruwa ta yi karin haske dangane da sauyi da aka samu a shugabancinta
- Rundunar sojin ruwan ta yi watsi da rahotannin da ke yawo cewa tsohon shugaban rundunar da aka sauke, Awwal Gambo ya ki mika mulki ga magajinsa, Emmanuel Ogalla
- A ranar Litinin, 19 ga watan Yuni ne shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wa shugabannin tsaron kasar ritaya tare da maye gurbinsu da sababbi
Hedkwatar rundunar sojin ruwa ta karyata zargin cewa shugaban rundunar mai barin gado, Awwal Gambo, ya ki mika mulki ga magajinsa, Emmanuel Ogalla, jaridar Premium Times ta rahoto.
A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni, daraktan labarai na rundunar sojin ruwa, Adedotun Ayo-Vaughan, mika mulki ga wani a rundunar soji yana da tsari.
A ranar Litinin ne shugaban kasa Bola Tinubu ya nada Mista Ogalla a matsayin sabon shugaban rundunar sojin ruwa.
Akwai tsari wajen mika shugabanci a rundunar sojin ruwa
Mista Ayo-Vaughan ya bayyana rahotannin da wasu kafafen yada labarai na yanar gizo suka fitar a matsayin kanzon kurege, yaudara da kuma yada labaran karya ga jama'a.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce:
"Saboda haka akwai bukatar jawabi kai tsaye.
"Bikin mika shugabanci ko karbar shugabanci yana da tsari tun daga farko a rundunar sojin ruwan Najeriya.
"Da zaran an sanar da sauyi a shugabanci, ana sa ran CNS mai barin gado ya bayar da cikakken bayanai ga CNS mai jiran gado, zagayawa da shi manyan wuraren rundunar sojin ruwa da kuma gudanar da bikin saukar da tuta.
"Saboda haka, an fara bikin da zai kai ga mika mulki da karbar mulki a hukumance za a kammala a ranar Juma'a, 23 ga watan Yuni, daidai da al'adar rundunar sojin ruwa."
Kakakin rundunar sojin ruwan ya bukaci jama'a da su yi watsi da rahoton karyan wanda yake hasashe ne na mawallafinsa.
Sabon shugaban hafsan soji: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Janar Lagbaja
A wani labarin, Legit.ng ta kawo a baya cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Janar Taoreed Abiodun Lagbaja a matsayin sabon shugaban hafsan sojojin Najeriya a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni.
Ana ganin Janar Lagbaja na daya daga cikin janarori da suka san kan aiki sosai a rundunar sojojin Najeriya.
Asali: Legit.ng