Biloniya Na Neman Mai Kula Da Karnukansa 2, Ya Shirya Biyan Albashi Miliyan N8 Duk Wata
- Ya zama dole masu neman aikin rainon karen su kasance da ilimi na musamman kan yadda za su ba karnukan kulawa
- Su za su dauki nauyin ba karnukan magunguna da aka rubuta masu da kuma kiyaye cikakkun bayanan lafiyarsu
- Bugu da kari, za su tsara lokacin motsa jiki ga kowani kare, sannan su tabbatar da ganin sun sami muhimman abubuwan da zai kara masu lafiyar jiki da na kwakwalwa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wasu hamshakan iyalan Amurka masu ji da kudi da ke zama a Landan suna neman mai raino da zai dunga kula da karnukansu guda biyu.
Biyawa karnukan bukatunsu
Wanda ya yi nasarar samun aikin zai kwashi albashi na zunzurutun kudi har naira miliyan 96.1 a shekara.
Iyalan sun wallafa tallar daukar aikin a Fairfax and Kensington, wata hukumar daukar aiki da ta shahara wajen nemawa masu hannu da shuni ma'aikata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
New York Post ta rahoto cewa wannan shine karo na farko da hukumar ke tallata aikin kula da kare.
Iyalin na zama ne a Knightsbridge, daya daga cikin wurare mafi tsada a birnin.
A cewar wata wallafa a LinkedIn, dole duk wanda zai nemi aikin ya shirya yin aiki a lokuta daban-daban, ciki harda yammaci, karshen mako, da kuma lokutan hutu. Wannan bukata na da matukar muhimmanci domin biyawa karnukan bukatunsu da kuma yin daidai da jadawalin iyalin.
Dunn ya kara da cewar:
"Akwai hutun makonni shida duk shekara, amma idan kana aiki da irin wadannan mutane, idan suna son zuwa Monaco gobe, za ka kasance a jirgi tare da wadannan karnukan."
A cewar mai daukar aikin, mutanen sun jaddada aniyarsu ta yin hidima mai inganci sannan kuma a shirye suke su biya da kyau, musamman idan ya shafi karnukan mafi soyuwa a garesu.
"Idan kudi ba matsala bane, mutane na son abu da ya fi kowanne kyau, kuma za ka ja hankalin mai kyau ne da albashi mai tsoka," inji shi.
Bidiyon matashiya da ke tuka babbar mota sanye da hijabi ya ba da mamaki
A wani labari na daban, wani bidiyon TikTok na wata matashiya Musulma sanye da hijabinta tana tuka babbar mota hankali kwance ya ja hankali a soshiyal midiya.
Bidiyon ya nuna banbanci mai ban mamaki tsakanin shigarta da babbar motar yayin da ta hau kujerar direba sannan ta tayar da motar.
Asali: Legit.ng