Majalisar Dokokin Jihar Benue Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi 23

Majalisar Dokokin Jihar Benue Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi 23

  • Majalisar dokokin Benue ta ba da shawarar dakatar da shugabannin kananan hukumomi 23 na jihar
  • Hakan ya biyo bayan bankado wasu badakaloli na kudade da kwamitin majalisar ya yi yayin da yake binciken rahoton kudaden shiga da wadanda suka fita daga asusun hukumomin
  • A cewar majalisar, dakatar da ciyamomin zai ba da damar yin bincike yadda ya kamata ba tare da tangarda ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benue - Majalisar dokokin jihar Benue ta bayar da shawarar dakatar da shugabannin kananan hukumomi 23 a jihar a ranar Laraba, 21 ga watan Yuni kan zargin karkatar da kudade.

Kakakin majalisar, Aondona Dajoh, ne ya sanar da shawarar a yayin zaman majalisar bayan ya duba rahoton kwamitin wucin gadi da aka kafa domin binciken rahoton kudaden shiga da kudaden da aka kashe wanda gwamnan ya gabatar masa.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali a Kano Yayin da 'Yan Daba Suka Tsiri Sabon Salon Rashin Mutunci a Kauyuka

Majalisar jihar Benue
Majalisar Dokokin Jihar Benue Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomi 23 Hoto: Punch
Asali: UGC

Dajoh ya bayyana cewa dakatarwar ya zama dole domin majalisar ta samu damar gudanar da bincike da kyau a kan kudaden shiga da kudaden da hukumomin suka kashe, rahoton Vanguard.

An tafka gagarumin barna a asusun kananan hukumomin, majalisa

Yan majalisar sun kuma yanke shawarar kara wa'adin binciken domin ya kunshi wa'adin kananan hukumomin yayin da suka bayyana cewa rahotannin watanni uku na abun da hukumomin suka kashe ya nuna an tafka gagarumin barna a asusun hukumomin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da farko, shugaban kwamitin wucin gadin, Peter Ipusu, ya bayyana cewa sun gano wasu makudan kudade da kananan hukumin 23 suka yi almubazaranci da su a jihar.

Saboda haka daga cikin abubuwan da suka bayar da shawara harda neman majalisar ta mika shawara da ke kira ga gwamnan ya dakatar da dukkanin hukumomin domin bayar da damar bincike da kai a kan kudaden hukumomin.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Tsige Duk Masu Kula da Hukumomi, Cibiyoyi da Kamfanonin Gwamnati

Ipusu ya bayar da shawarar ne kasa da awanni 24 bayan majalisar ta kafa kwamitin mutum uku a ranar Talata domin gudanar da bincike kan kudaden shiga da kudaden da aka kashe na kananan hukumomi 23 a jihar, Daily Trust ta rahoto:

Ana za ran kwamitin karkashin jagoranci mamba mai wakiltan mazabar Katsina Ala, Peter Ipusu da Manger Manger na mazabar Tarka da Cyril Ekong, mai wakiltan mazabar Oju II za su gudanar da gagarumin bincike.

Manyan mutane ke azabtuwa da tsadar mai ba talakan Najeriya ba, tsohon dan majalisa

A wani labari na daban, tsohon dan majalisar wakilai, Musa Adar, ya ce karin farashin man fetur da aka yi sakamakon cire tallafin man fetur ya fi shafar manyan mutane fiye da talakawan Najeriya.

Mista Adar, wanda ya wakilci mazabar Gada-Goronyo a jihar Sokoto tsakanin 2007 da 2023, ya ce abun ya fi shafar manyan mutane fiye da talakawan Najeriya saboda sun fi kowa siyan man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: