Gwamna Otu Ya Haramta Aikin Acaba a Babban Birnin Jihar Cross River
- Gwamna Bassey Otu na jihar Kuros Ribas ya haramta ayyukan 'yan acaɓa a cikin kwaryar birnin Kalaba, babban birnin jihar
- A wata sanarwa da gwamnatinsa ta fitar ranar Laraba, gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne bayan zaman neman shawara da hukumomin tsaro
- Ya kuma gargaɗi duk wasu da ke ruguza kadarorin gwamnati da su gaggauta tuba tun kafin lokaci ya kure musu
Cross River - Gwamnan jihar Kuros Riba, Sanata Bassey Otu, ya bada umarnin haramta amfani da baburan haya waɗanda aka fi sani da 'yan Acaɓa a cikin kwaryar birnin Kalaba.
Rahoton Channels tv ya tattaro cewa wannan matakin na ƙunshe a wata sanarwa da Sakataren watsa labaran gwamna, Emmanuel Ogbeche, ya fitar ranar Laraba.
Ya ƙara da bayanin cewa gwamna bai ɗauki wannna matakin bisa son ransa ba, sai da ya nemi shawarwarin shugabannin hukumomin tsaro na jihar.
A cewar sanarwan, duk mai son amfani da Babur ɗinsa domin samun na cefane ba'a hana shi amma ya nufi can gefen gari, ba cikin cibiyar Kalaba, babban birnin jihar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane mataki gwamnati zata ɗauka kan duk wanda ya karya doka?
Gwamnatin jihar Kuros Riba ta kuma gargaɗi jama'a cewa duk wanda ta kama ya karya wannan doka zata kwace Babur ɗinsa kuma zata gurfanar da shi a gaban Kotu.
PM News ta rahoto sanarwan ta ce:
"Mai girma gwamna, Sanata Bassey Otu, bayan neman shawara daga shugabanni hukumomin tsaro, ya haramta ayyukan 'yan Acaba a cikin kwaryar birninn Kalaba."
"Duk masu neman abinci ta hanyar aikin Acaɓa an ƙayyade nusu su yi sana'arsu a Anguwannin gefen gari nesa da cibiyar birni."
Bugu da ƙari gwamnatin Otu, mamban APC, ta gargaɗi mutane su guji ruguza kadarorin gwamnati, kama daga Fitilun kan titi, Na'urar ba da hannu da sauransu.
Ta kuma shawarci duk masu hannu a aikata manyan laifuka su tuba tun lokaci bai ƙure ba domin wanda ya shiga hannu zai ɗanɗana kuɗarsa a hannun doka.
Gwamna Nwifuru Na Ebonyi Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni 35
A wani rahoton na daban kuma Gwamnan jihar Ebonyi ya rantsar da sabbin kwamishinoni 35 da wasu muƙarrabansa da ya naɗa.
Gwamnan ya umarci su haɗa karfi wajen ciyar da jihar zuwa gaba domin ba bu wanda ya ɗauko saboda siyasa.
Asali: Legit.ng