Jerin Sunayen Masu Kudin Afrika 10 Yayin da Dan Afrika Ta Kudu Ya Kwace Matsayin Dangote
- Aliko Dangote ya rasa matsayinsa a matsayin mai kudin Afrika inda wani biloniyan Afrika ta Kudu Johann Ruper ya maye gurbinsa
- Rupert ya yi nasarar maye gurbin Dangote ne saboda faduwar darajar naira a Najeriya
- Aliko Dangote ya shafe kimanin shekaru 10 a kan wannan matsayi na mai kudin Afrika
Karyar da darajar Naira da Babban Bankin Najeriya ya yi, ya shafi arzikin Aliko Dangote, inda hakan ya baiwa biloniyan Afrika ta Kudu Johann Rupert damar maye gurbinsa a matsayin mai kudin Afrika.
Binciken Legit.ng ya nuna cewa a watan Yunin 2023, arzikin Dangote ya tsaya a biliyan $14.2, idan aka kwatanta da biliyan $11.1 na Rupert.
Ana tsaka da fama da faduwar darajar Naira, wanda a kansa ne arzikin Dangote yake, sai biloniyan Najeriya ya fadi zuwa na biyu a jerin masu kudin Afrika, yayin da Rupert ya koma na daya.
Forbes ta rahoto cewa zuwa safiyar Litinin, 19 ga watan Yunin 2023, Dangote ya rasa fiye da dala biliyan 4 na arzikinsa kuma yanzu arzikinsa na kan dala biliyan 10.7.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A daya bangaren, arzikin Rupert ya karu zuwa dala biliyan 12.0, kuma tazarar na iya karuwa a kwanaki masu zuwa.
Jerin sunayen manyan biloniya 10 a Afrika, arziki da kasarsu
Ga jerin sunayen manyan biloniya 10 a Afrika zuwa ranar Litinin, 19 ga watan Yunin 2023 kamar yadda Forbes ta rahoto.
Biloniya | Arzikin | Kasa |
Johann Rupert | $12bn | Afrika Ta Kudu |
Aliko Dangote | $10.7bn | Najeriya |
Nicky Oppenheimer | $8.4bn | Afrika Ta Kudu |
Nassef Sawiris | $6.9bn | Masar |
Abdulsamad Rabiu | $6.2bn | Najeriya |
Issad Rebrab | $4.6bn | Algeria |
Mike Adenuga | $4.3bn | Najeriya |
Mohamed Mansour | $3.6bn | Masar |
Naguib Sawiris | $3.3bn | Masar |
Patrice Motsepe | $2.6bn | Afrika Ta Kudu |
Tattalin arziki da wasu bangarori 3 da Tinubu ya kwankwasa cikin makonsa na 3 a matsayin shugaban kasa
A wani labarin, mun ji cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya ci gaba da ba yan Najeriya mamaki tun bayan da ya kama aiki a matsayin shugaban Najeriya a ranar 29 ga watan Mayu.
Da ake duba ayyukan shugaban kasar cikin makonsa na uku a matsayin shugaban kasar Najeriya, Tinubu ya aiwatar da manyan manufofi da matakan da suka sauya abubuwa a bangarori daban-daban na kasar.
Asali: Legit.ng