‘Yan Bindiga Sun Yi Ta’adi Cikin Dare a Kaduna, Sun Harbe Basarake Da ‘Ya ‘Yansa 4
- Ardon birnin Zazzau da kuma kewaye ya na barzahu a dalilin ta’adin wasu miyagun ‘yan bindiga
- A karshen makon nan wasu su ka shiga har cikin gida, su ka bindige Alhaji Shuaibu Mohammed
- Bayan Ardo da aka kashe, an hallaka manyan yaransa hudu wanda tun tuni aka yi jana’izar dukkansu
Kaduna - Wasu miyagu da ake zargin ‘yan bindiga ne, sun hallaka Ardon Birni da Kewayen Zazzau, Alhaji Shuaibu Mohammed da wasu iyalinsa.
Rahoton da aka samu daga The Guardian a ranar Lahadi, ya tabbatar da cewa ‘yan bindigan sun kashe Shuaibu Mohammed a wani harin da su ka kai.
Wannan mummunan lamari ya auku ne da kimanin karfe 10:00 na dare a ranar Asabar a kauyen Dorayi a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna.
An kashe wasu 'ya 'yansa 4
Baya ga hallaka Ardon Birni da Kewayen Zazzau, ‘yan bindigan sun kashe ‘ya ‘yansa hudu wanda kowane daga cikinsu ya na da aure da kuma iyalinsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Punch ta ce miyagun da su ka zo su biyar, sun sace shanu 100 daga gidan marigayin.
Daily Nigerian ta rahoto mai dakin Ardo, Halima Shuaibu, ta na fadawa manema labarai cewa an birne wadannan Bayin Allah su ka riga mu cikawa.
"An fito da Ardo daga cikin dakinsa sai aka harbe shi sau biyu a kai, a nan take ya mutu.
‘Yan bindigan sun rika shiga daki bayan daki a gidan, su ka hallaka ‘ya ‘yana hudu wadanda su na da aure da kuma ‘ya ‘yan kan su.
Wadanda aka kashe su ne: Adamu Shuaibu, Musa Shuaibu, Abubakar Shuaibu da Ibrahim Haruna.
A cikin ‘ya ‘yan marigayin, Abdurrahman Shuaibu ya shaida cewa ‘yan bindigan sun hallaka wasu mutane biyu yayin da su ke fita daga kauyen na su."
- Malama Halima Shuaibu
Da aka tuntubi mai magana da yawun bakin ‘yan sanda na reshen jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya ce bai da wata masaniya a game da harin.
Shirin hajjin bana
A gefe guda, kun ji labari cewa akwai mutane da-dama da sun biya kudin hajji, amma ba su makomarsu ba yayin da aka shiga watan Zul Hajji.
Akwai kamfanin jirgin da ke da fasinjoji 7, 000, amma har yanzu mutum 300 ya dauka. Muddin ba dauki mataki ba, ‘yan Najeriya za su rasa hajji.
Asali: Legit.ng