“Mata Sun Cancanci Karin Mukaman Shugabanci” - Inji Uwargidan Shugaban Kasa
- Matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta magantu a kan bukatar sanya mata a harkokin shugabanci
- Misis Tinubu, ta bayyana cewa mata sun cancanci a basu karin mukaman shugabanci domin bayar da gudunmawa wajen ci gaban kasar
- Ta bayyana haka ne a wajen taron kaddamar da wani littafi na kungiyar matan sojoji a Abuja
Uwargidan shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa ya bai kamata a mayar da matan Najeriya kashin baya ba, maimakon haka kamata ya yi a basu karin mukaman shugabanci domin bayar da gudunmawa wajen ci gaban kasar.
Oluremi ta fadi hakan ne a Abuja yayin kaddamar da wani littafi da matar shugaban hafsan soji, Misis Salamatu Yahaya, ta yi, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Matar shugaban kasar wacce ta samu wakilcin Sanata Nora Daduut, ta ce:
"Ya kamata a sake duba yawan mata a mukaman shugabanci sannan a kara shi kuma littafin zain taimaka sosai wajen inganta rayuwa ba wai ga mambobin kungiyar NAOWA ba kawai harma ga matan Najeriya."
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A jawabinta, marubuciyar littafin kuma shugabar kungiyar matan sojoji ta ce ta rubuta littafin ne a kokarin ganin mata sun shiga harkar shugabanci.
Ta ce:
“Karfafa labaran NAOWA da daukacin matan Najeriya na da matukar muhimmanci musamman a mukaman shugabanci domin matan Najeriya na da muhimmiyar gudunmawar da za su bayar wajen ci gaban kasar.
"Littafin zai zama tushen ginawa a kan manyan nasarorin matan Jami'an Sojojin Najeriya da matan Najeriya da ke ci gaba da kafa tarihi a wuraren aikinsu."
A taimaka a bamu mukamin ministan babban birnin tarayya, Yan asalin Abuja sun roki Tinubu
A wani labarin kuma, yan asalin babban birnin tarayya Abuja sun mika kokon bararsu a gaban shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu, inda suka bukaci ya taimaka ya ba dan cikinsu mukamin ministan babban birnin tarayya Abuja.
Yan yankin sun ce sun gaji da yaudarar da cutar da ake yi masu na dauko yan waje ana daurawa kan kujerar domin jibantar lamuransu.
A cewarsu mai daki shine ya san inda yake masa yoyo, inda suka ce babu yadda za a yi wanda ya zo daga waje da bai fahimci halin da suke ciki ba ya iya magance masu matsalolinsu.
Asali: Legit.ng