Matashiya Ta Dafa Kwai Karo Na Farko A Rayuwarta, Ya Fito Kamar Bayan Tukunya a Bidiyo

Matashiya Ta Dafa Kwai Karo Na Farko A Rayuwarta, Ya Fito Kamar Bayan Tukunya a Bidiyo

  • A wani bidiyo mai ban dariya, wata matashiya yar masu hannu da shuni ta yi kokarin dafa kwai karo na farko a rayuwarta, amma aka yi rashin dace
  • Bidiyon ya nuno ta rike da konannen kwai a hannunta, tana mai bayyana yadda ta dafa shi
  • Cikin yanayi na barkwanci, ta ba mutane shawarar yadda za su dafa nasu, tana mai cewa da zaran mutum ya zuba ruwa a wuya ya saka kwan sai ya yi baccinsa

Wani bidiyon ban dariya ya yadu a TikTok, inda wata matashiya yar masu hannu da shuni ta yi kokarin dafa kwai karo na farko a rayuwarta, amma sai aka yi rashin dace domin dai kwan ya babbake fiye da tunani.

Rike da konannen kwai a hannunta, matashiyar cike da barkwanci ta bayyana yadda ake dafa irin kwanta: "Kawai ka zuba ruwa a kan wuta, sai ka saka kwan a ciki, sannan ka yi bacci."

Kara karanta wannan

Biyu Babu: Bakano Ya Yi Karyar Garkuwa Da Kansa, Barayi Sun Sace N356k Da Ya Karba Na Fansa

Matashiya rike da konannen kwai
Matashiya Ta Dafa Kwai Karo Na Farko A Rayuwarta, Ya Fito Kamar Bayan Tukunya a Bidiyo Hoto: @twinzloves
Asali: TikTok

Nan take bidiyon ya haddasa cece kuce, yayin da masu kallo suka kasa boye dariyarsu kan wannan kwamacala da ta dafa da sunan kwai.

Ta nunawa duniya konannen kwai da ta dafa cike da kwarin gwiwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bugu da kari, ta kuma yi ikirarin cewa mahaifiyarta ta kara kudin sadakinta saboda wannan lalataccen girki da ta yi.

Jama'a sun yi martani

Mutane da dama da suka ci karo da bidiyon sun tofa albarkacin bakunansu inda suka dunga yi mata ba'a cewa ta yi kokari harma wani ya ce sadakinta ya tashi zuwa biliyan 1.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@praiseudeogu2: '

"Hilda Baci ta biyu."

@only_one_jhummight ta ce:

"Ci gaba da wasa."

@lizzycouture50 ta ce:

"Awwwwn girki mai kyau☺️."

@lizzylizzyshow ta yi bayani

"Gasasshen Egg." KIN YI KOKARI DAN ALLAH."

Kara karanta wannan

"Sun Yanke Hulda Dani": Magidanci Ya Yi Karyan Ya Mutu, Ya Isa Wajen Jana'izarsa a Jirgi Mai Saukar Ungulu

@itz_hanny7:

"A zahirin gaskiya kin yi kokari sosai sadakinki naira biliyan 1 ne."

Kalli bidiyon a kasa:

Amarya da ango sun keta daji da kafa zuwa wajen daurin aurensu

A wani labarin kuma, wasu sabbin ma'aurata sun dauka hankali a soshiyal midiya bayan bidiyonsu ya bayyana inda aka gano su suna keta jeji a kafa zuwa wajen daurin aurensu.

An gano amarya da angon suna tafiya yayin da shi mijin ya taya ta daga rigarta ta baya don kada ya nadi datti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng