Hankula Sun Tashi Yayin Da EFCC Ta Gayyaci Tsofaffin Ministocin Buhari 8, Cikakkun Bayanai Sun Fito
- Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), ta ƙaddamar da bincike kan ayyukan da wasu tsofaffin ministocin gwamnatin Buhari suka gudanar lokacin da suke rike da mukamansu
- Wani rahoto na nuni da cewa jami’an da ke gudanar da binciken, sun tattara wasu ƙwararan hujjoji a kan tsofaffin ministocin da abin ya shafa
- Wata majiya mai tushe ta ce baya ga tsohuwar ministar harkokin mata, Pauline Tallen, akwai ƙarin wasu bakwai da hukumar EFCC ta gayyaci
FCT, Abuja – Rahotanni na nuni da cewa, Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC), na binciken wasu daga cikin tsofaffin ministoci takwas, waɗanda suka yi aiki a lokacin tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari .
A rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa a ranar Juma’a, 16 ga watan Yuni, an gayyaci waɗannan ministocin ne bisa zargin aikata laifuka na cin hanci da rashawa.
Katunan gayyatar sun buƙaci tsofaffin ministocin da su yi bayanin yadda suka kashe kuɗaɗen da aka warewa ma’aikatunsu domin gudanar da ayyuka a lokacin da suke riƙe da muƙaman gwamnati.
EFCC na binciken ministocin Buhari
An tattaro cewa an miƙa takardun gayyatar ne gabanin dakatar da Abdulrasheed Bawa a matsayin shugaban hukumar.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Wani babban jami’in hukumar ta EFCC, wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa, baya ga tsohuwar ministar harkokin mata, Pauline Tallen da aka gayyace ta a makon da ya gabata bisa zargin almundahanar Naira biliyan 2, an kuma gayyaci ƙarin wasu ministocin bakwai.
EFCC ta gayyaci tsohon Attoni janar Abubakar Malami? Gaskiya ta bayyana
A baya Legit.ng ta rahoto cewa, tsohon ministan shari’a kuma Anttoni janar na gwamnatin tarayya (AGF), Abubakar Malami, ya karyata rade-radin da ake yadawa cewa hukumar EFCC ta gayyace shi.
Malami ya kuma ce ba ya yunƙurin tserewa daga Najeriya, kuma a shirye yake ya amsa tambayoyi idan akwai bukatar hakan.
Kashim Shettima ya nemi afuwar kan kalaman da ya yi
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya nemi afuwar Musulmin Najeriya kan kalaman da ya yi a cikin 'yan kwanakin nan.
An ruwaito Shettima yana faɗin wasu kalamai da suka harzuƙa Musulmin Najeriya, a yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaɓen Majalisar Dattawan Najeriya.
Kashim Shettima ya bayyana cewa jama'a basu fahimci kalaman nasa a daidai ba, inda ya nemi duk wanda ya ɓatawa rai da ya yi haƙuri.
Asali: Legit.ng