Abubuwa 5 da Bola Tinubu Ya Ambata a Jawabinsa na Farko a Ranar Damukaradiyya

Abubuwa 5 da Bola Tinubu Ya Ambata a Jawabinsa na Farko a Ranar Damukaradiyya

  • A yau ne aka ji jawabin da Bola Ahmed Tinubu ya yi wa ‘Yan Najeriya domin bikin damukaradiyya
  • Tun bayan maganar da ya yi a wajen rantsar da shi, sai a yau shugaban Najeriya ya yi jawabi
  • Mai girma Bola Tinubu ya yi maganar zaben 1993 da siyasar Najeriya a jawabin da ya gabatar

Legit.ng Hausa ta tattaro manyan kanun jawabin shugaban na Najeriya tun daga maganar zaben 1993 zuwa cire tallafin man fetur da aka yi.

Tinubu ya ce mulkin farar hula na cin albarkacin Kudirat Abiola, Pa Alfred Rewane da Shehu Yar’Adua ne. Daily Trust ta kawo cikakken jawabin.

Bola Tinubu
Shugaban Kasa, Bola Tinubu a taro Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

1. Zaben Abiola

Shekaru 30 kenan yau da ‘Yan Najeriya su ka je filin zabe domin zaben shugaban kasar da su ke so ya dawowa mutane mulki daga hannun sojoji.

Kara karanta wannan

Bayan Ganawa da Tinubu, Gwamnan APC Ya Faɗi Sanatan da Zai Zama Shugaban Majalisar Dattawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashe nasarar Moshood Kashimawo Olawale na jam’iyyar SDP ya samu a zaben da ya fi kowane adalci da gaskiya, ya dasa cibiyar mulkin farar hula.

2. Sauran gwarazan damukaradiyya

A duk rana irin ta yau a tsawon shekarun nan, mu na tunawa da sauran shahidan damukaradiyya irinsu Kudirat Abiola da aka yi wa kisan gilla wajen kare al’umma.

Mu na tunawa da Pa Alfred Rewane wadanda suka yi yakin karbo ‘yanci da Janar Shehu Musa Yar’Adua (rtd) da sojojin su ka rufe masu baki a gwagwarmayar.

3. Takarar shugaban kasa

Yadda aka gwabza wajen yakin zabe ya nuna irin gawurtar da damukaradiyya tayi a kasar nan. Sunnar siyasa ce wasu za su ci zabe alhali wasu kuma za su fadi.

Dadin damukaradiyya ita ce akwai damar sake shiga takara wata rana. Wadanda ba za su iya jurewa dacin faduwa ba, ba su cancanta da samun nasarar zabe ba.

Kara karanta wannan

Ranar Damokradiyya: Shehu Sani Ya Saki Jerin Sunayen Yan Arewa Da Suka Yi Fafutukar June 12

4. Tinubu zai bi dokar kasa da shari’a

Yayin da Bola Tinubu ya bukaci wadanda aka tika da kasa a zaben bana su nemi hakkinsu ta hanyar da tsarin mulki ya yi tanadi, ya tabo batun bin dokar kasa.

Shugaban kasar ya nuna muhimmacin bin doka da samar da Alkalan da za su yi shari’an adalci, a dalilin haka ya ce an soma gyara da kara shekarun ritayar Alkalai.

5. Buhari da tallafin fetur

Kamar yadda jaridar ta rahoto, Mai girma Tinubu ya ce ya bi tafarkin wanda ya gada watau Muhammadu Buhari wajen cire tallafin fetur bayan ya hau kan karaga.

Ina kira a gare ku da ku sadaukar da rayuwarku kadan domin kasarmu ta dore. In tabbatar maku da cewa yarda da mu da ku ka yi, ba zai tafi a banza kurum ba.

Gwamnatin nan za tayi maku sakayya ta hanyar gagarumin kashe kudi a harkar sufuri, ilmi, inganta wuta lantarki, kiwon lafiya da sauran abubuwan more rayuwa.

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Fadi Yadda Zai Rage Radadin Tashin Fetur, Ya Yabi Abiola da 'Yar'adua

Tallafin fetur ya tafi

A baya rahoto ya za inda aka ji Bola Tinubu ya ce janye farashin tallafin fetur ya zama dole, ya sha alwashin gyara wuta, ilmi da asibitoci a madadin saukin fetur.

Sabon shugaban Najeriya ya yabi gwagwarmyar mazajen baya wanda su ka yi gwamnatin sojin da ta hana MKO Abiola zama shugaban Najeriya a 1993.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng