Shettima Ya Kaddamar Da Masallacin Majalisar Dokoki Na Miliyan N570
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kaddamar da babban masallacin majalisar dokokin tarayya
- An bude babban masallacin ne a ranar Juma'a, 2 ga watan Yuni inda Shettima ya wakilci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
- Shettima ya yi kira ga shugabanni da su zamo masu kan-kan da kai domin wata rana za a bar duniya
Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya kaddamar da ginin Masallacin Juma'a da al'ummar Musulmi suka gina a majalisar dokokin tarayya.
Shettima wanda ya wakilci Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a taron ya yi kira ga shugabanni da su yi tawali’u yayin da suke sauke nauyin da ya rataya a wuyansu a lokacin da suke rike da madafun iko sannan su nemi lahirarsu ta hanyar irin wadannan ayyuka da sadaka.
A bi mulki da duniya a sannu don ba matabbata bane, Shettima
Shettima ya ce ya kamata su kuma lura da mulki da rayuwa domin dole wata rana su bar mukamansu da ma duniyar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya ce ya tattara kayayyakinsa daga tsohon ofishinsa a matsayin sanata yana mai cewa, cikin mako biyu, mutane da dama ba za su san cewa ya taba zama a ofishin ba wanda ya ce ya tabbatar da mulki ba matabbata bane.
Ya ce:
"Shekaru 50 daga yanzu, yawancinmu ba za su kasance a raye ba. Mu yi aiki cike da tawali'u; mulki da dukiya kyauta ne daga Allah."
Da yake magana a taron, shugaban kwamitin aiki na masallacin majalisar dokokin, Sanata Ibrahim Shekarau ya ce shugabancin kwamitin majalisar dattawa da na wakilai da aka kafa ne suka yi tunanin gina masallacin a 2021.
Allah ne ya nufi yan majalisa ta tara za su gina masallacin, Sultan na Sokoto
A nashi jawabin, Sultan na Sokoto, Muhammad Sa'ad Abubakar, wanda ya samu wakilcin sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya yaba ma dukkanin mutanen da suka bayar da gudunmawa wajen gina masallacin, cewa Allah ne ya nufi yan majalisar dokoki na 9 da yin haka.
Cire tallafin mai: Gwamnatin Tinubu za ta hadu da matsala, Malamin addini
A wani labarin kuma, mun ji cewa shahararren malamin nan na Najeriya, Primate Elijah Ayodele ya soki cire tallafin mai da gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu ta yi.
Primate Ayodele ya ce yanzu ya yi wuri da Tinubu zai dauki wannan mataki inda ya hangowa gwamnatinsa gagarumin matsala a gaba.
Asali: Legit.ng