EFCC Ta Titsiye Tsohuwar Ministar Buhari Kan Karkatar Da N2bn
- Jami'an hukuma EFCC sun tsare tsohuwar ministar harkokin mata da tambayoyi kan zargin wawure kudi naira biliyan 2
- Tsohuwar mistar Buhari, Pauline Tallen, ta isa ofishin EFCC na Abuja da safiyar Alhamis, 1 ga watan Yuni
- Zuwa yanzu babu wani cikakken bayani game da kudaden da ake tuhumarta da karkatarwa
Abuja - Hukumar yaki da cin hanci da hana yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC) ta tsitsiye tsohuwar ministar harkokin mata, Pauline Tallen, kan zarginta da aikata rashawa, jaridar The Cable ta rahoto.
An tattaro cewa Tallen ta isa ofishin hukumar na Abuja a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuni domin amsa tambayoyi kan karkatar da kudi naira biliyan 2.
Channels TV ta rahoto cewar jami'an bincike na hukumar yaki da cin hanci da rashawar sun ci gaba da yi wa tsohuwar ministar da ta isa ofishin nasu da misalin 12:00 na rana tambayoyi har zuwa karfe 8:00 na dare.
Yanzu Yanzu: Kungiyar Kwadago Ta Yi Barazanar Shiga Yajin Aikin Gama Gari, Ta Ba Gwamnatin Tinubu Sabon Wa’adi
Koda dai babu wani cikakken bayani kan zargin da ake mata zuwa lokacin kawo wannan rahoton, wata majiya da ke sane da lamarin ta bayyanawa Channels TV cewa a kan batun wawure naira miliyan 2 ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin Tallen da karkata da kudin shirin wanzar da zaman lafiya na matan shugabannin Afrika
An yi zargin cewa an karkata da wani bangare na kudin ne daga shirin wanzar da zaman lafiya na matan shugabannin kasashen Afrika.
Ba a samun jin ta bakin kakakin hukumar, Wilson Uwujaren, don tabbatar da lamarin ba.
EFCC ta tsare tsohon gwamnan APC da tambayoyi kan wawure N4bn
A wani lamari makamancin wannan, mun ji cewa jami'an hukumar EFCC sun titsiye tsohon gwamnan jihar Ekiti, Dr Kayode Fayemi bisa zargin halasta kuɗin haram kimanin naira biliyan N4bn.
An dai tattaro daga majiya cewa Fayemi ya isa Ofishin EFCC da ke Ilorin, babban birnin jihar Kwara da misalin 9:40 na safiyar Alhamis.
Labari Da Duminsa: Tinubu Ya Sanar Da Nadin Gbajabiamila A Hukumance, Tsohon Mataimakin Gwamnan Jigawa Ya Samu Mukami Shima
Awatan Mayu, Fayemi ta hannun lauyansa, Adeola Omotunde, SAN, ya roki EFCC ta jinkirta masa ya gabatar da littafin girmamawa Buhari
Ya ce bayan gabatar da wannan littafi da ya rubuta, zai amsa gayyatar da hukumar ta masa domin amsa tambayoyi kan zargin halastawa kansa kuɗin haram.
Asali: Legit.ng