Matan Shugaban Kasa Sun Cancanci A Musu Tagomashin Alkhairi Bayan Sauka Mulki, Aisha Buhari

Matan Shugaban Kasa Sun Cancanci A Musu Tagomashin Alkhairi Bayan Sauka Mulki, Aisha Buhari

  • Matar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ta bayyana kulawa ta musamman da ya kamata matan shugaban kasa su samu bayan barin ofis
  • Aisha ta ce ya kamata matan shugaban kasa su samu alfarma kamar irin na mazajensu ko shugabannin da ke mulki
  • Uwargidar shugaban kasar ta bayyana hakan a ranar Juma'a, 26 ga watan Mayu a wajen kaddamar da wani littafi a Abuja

Matar shugaban kasa mai barin gado, Aisha Buhari, ta yi kira da a dunga yi wa matan shugaban kasa tagomashin alkhairi idan suka sauka daga karagar mulki.

A cewar Aisha, ya kamata matan shugaban kasar su dunga samun alfarma irin na tsoffin shugabannin kasa kamar ba su ababen hawa, daukar nauyin kula da lafiyarsu da kuma basu yan alawus sabanin yadda abun yake a yanzu, vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu Ba Zai Hakura Ba, Ya Fadi Abinda Zai Wa Buhari Ko Da Ya Gudu Daura Ko Nijar

Matar shugaban kasa, Aisha Buhari
Matan Shugaban Kasa Sun Cancanci A Musu Tagomashin Alkhairi Bayan Sauka Mulki, Aisha Buhari Hoto: Aisha Buhari
Asali: Facebook

Aisha ta ce matan shugabannin kasar sun cancanci wannan alfarma kamar mazajensu saboda a duk lokacin da matsin lamba ya zao, babu wanda ke son sanin ko ka fita daga villa ko baka fita ba, rahoton Sahara Reporters.

Matan tsoffin shugabanni sun cancanci kulawa ta musamman, Aisha Buhari

Uwargidar shugaban kasar ta yi magana ne a wajen kaddamar da wata takarda a Abuja wanda shugabar kungiyar matan tsaro da na yan sanda (DEPOWA), Misis Vickie Anwuli Irabor ta wallafa mai taken “The Journey of a Military Wife”.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Da take bayanin dalilin da yasa akwai bukatar yi wa matan shugabannin kasa wannan alfarmar, Misis Buhari ta ce:

"Na auri mijina a matsayin matar tsohon shugaban kasa. Zan tafi a yan kwanaki masu zuwa a matsayin matar tsohon shugaban kasa a karo na biyu.

Kara karanta wannan

Ofishin Matar Shugaban Kasa: Aisha Buhari Ta Mika Mulki Ga Magajiyarta, Remi Tinubu

"Ya kamata su duba mu a matsayin matan tsoffin shugaban kasa. Ya kamata su hada da matan tsoffin shugaban kasa, su bamu wasu alfarma da muka cancanci samu a matsayin matan tsoffin shugaban kasa, ba wai tsoffin shugabannin kasa kawai ba."

Ofishin matar shugaban kasa: Aisha Buhari ta mika mulki ga Remi Tinubu

A wani labarin, mun ji cewa Aisha Buhari ta mika ragamar ofishin matar shugaban kasa a hannun Remi Tinubu, matar zababben shugaban kasa.

A ranar 29 ga watan Mayu ne wa'adin mulkinsu zai kare inda shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu zai hau karagar mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: