Lokaci Ya Yi: Shugaban Riko Na Karamar Hukumar Karasuwa a Jihar Yobe Ya Rasu
- Allah ya yi wa shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Karasuwa da ke a jihar Yobe rasuwa bayan ƴar gajeruwar jinya
- Hon Lawan Gana ya riga mu gidan gaskiya ne bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar jinya a asibitin gwamnatin tarayya da ke Nguru
- Marigayin ya rasu ne yayin da ake dab da bikin rantsar da shugabannin riƙo na ƙananan hukumomin jihar Yobe
Jihar Yobe - Shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Karasuwa a jihar Yobe, Hon Lawan Gana, ya riga mu gidan gaskiya.
Hon Lawan Gana ya koma ga mahaliccinsa ne bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Babban darektan harkokin watsa labarai na gwamnan jihar Yobe, Mamman Muhammad, shine ya sanar da rasuwar Lawan.
Mamman Muhammad ya sanar da labarin rasuwar shugaban riƙon ne a wajen ƙaddamar da shirin bayar da tallafin sana'o'i da kwamishinan ma'aikatar samar da sana'o'i da bayar da tallafi na jihar ya shirya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa marigayi Gana ya rasu ne a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke a Nguru, bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar rashin lafiya.
Marigayin ya rasu ana dab da rantsar da su akan mulki
Ƙafin rasuwarsa, Gana ya riƙe muƙamin shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Karasuwa, har na tsawon wata shida, kafin gwamna Mai Mala Buni ya sauke su daga muƙamansu.
Daga an sake naɗa shi a matsayin shugaban riƙon ƙwarya na ƙaramar hukumar Karasuwa, cewar rahoton Daily Post.
Marigayi Lawan Gana yana daga cikin shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi 17 da za a rantsar da su a ranar Juma'a, 26 ga watan Mayun 2023.
Matashin Da Ya Ci Zaben Dan Majalisar Tarayya a Taraba Ya Rasu
A wani labarin na daban kuma, Allah ya yi wa wani matashi rasuwa wanda ya samu nasarar lashe zaɓen ɗan majalisar tarayya a jihar Taraba, da ke yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
Kafin komawarsa zuwa ga mahaliccinsa, Hon Isma'ila Maihanci ya lashe zaɓen ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Jalingo/Yorro/Zing a majalisar wakilai ta ƙasa.
Asali: Legit.ng