An Sauya Sunan Gadar Neja Ta Biyu Zuwa Sunan Shugaba Muhammadu Buhari

An Sauya Sunan Gadar Neja Ta Biyu Zuwa Sunan Shugaba Muhammadu Buhari

  • An canza sunan gadar Neja ta biyu zuwa sunan shugaban ƙasa mai barin gado Muhammadu Buhari
  • Gwamnonin kudu maso gabas ne suka yanke shawarar sauya sunan gadar zuwa 'Gadar Neja ta Biyu ta Muhammadu Buhari'
  • Shugaba Buharin ne ya kaddamar da gadar a ranar Talata, wanda ya halarci taron ta kafar sadarwa ta zamani

An canza sunan gadar Neja ta biyu da sunan shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wacce ya ƙaddamar a yau Talata ta kafar sadarwa.

Mataimaki na musamman kan harkokin sadarwar zamani ga shugaban ƙasa, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

An sanyawa gadar Neja ta biyu sunan shugaba Buhari
An sanyawa gadar Neja ta biyu sunan shugaba Muhammadu Buhari. Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Ya rubuta kamar haka:

“’Yan uwana maza da mata, a hukumance, yanzu muna da gadar MUHAMMADU BUHARI.”

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Da ɗumi-ɗumi: Gadar Neja ta Biyu za a kira ta da sunan 'GADAR NEJA TA BIYU TA MUHAMMADU BUHARI'.”

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Gwamnan APC Ya Samu Nasarar Zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa

Sai gwamnonin kudu maso gabas sun amince

Haka nan kuma, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin dijital da sabbin kafafen watsa labarai, Tolu Ogunlesi, shi ma ya tabbatar da sauya sunan gadar zuwa sunan Buhari a shafinsa na Tuwita.

Ya bayyana cewa sai bayan gwamnonin kudu maso gabas sun amince da sabon sunan sannan hakan ya tabbata.

"Yanzu wannan ne sunanta a hukumance, amma sai da amincewar gwamnonin kudu maso gabas da sauran masu ruwa da tsaki, a canza zuwa sunan Muhammadu Buhari (MMB),".

Tolu Ogunlesi, mai taimaka wa shugaba Buhari kan harkokin yaɗa labarai ya wallafa a shafin sa na Tuwita a ranar Talata:

"Bayan tuntubar junansu, gwamnonin kudu maso gabas sun amince a sauya sunan gadar Neja ta biyu zuwa gadar 'Neja ta biyu ta Muhammadu Buhari'."

Gwamnonin sun yi hakan domin yabawa Buhari

Premium Times ta samu bayanai cewa gwamnonin sun ɗauki matakin ne, domin yabawa shugaba Buhari bisa kammala aikin da gwamnatocin da suka shuɗe suka kasa yi.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Yanke Hukunci, Ta Baiwa Peter Obi Wa'adin Da Zai Gabatar da Shaidu Kan Nasarar Tinubu

Ejimofor Opara, mai taimakawa Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra ta fuskar yaɗa labarai, ya shaida wa manema labarai cewa, Ministan Wutar Lantarki na Najeriya, Babatunde Fashola, ya bayyana sauya sunan gadar a lokacin kaddamarwa.

Mista Opara, ya ce ministan ya bayyana cewa gwamnonin kudu-maso-gabas ne suka ɗauki matakin sauya sunan gadar zuwa sunan Buhari.

Gwamnonin biyar na kudu maso gabas sune, Charles Soludo (Anambra), Dave Umahi (Ebonyi), Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu), Hope Uzodinma (Imo) da kuma Okezie Ikpeazu (Abia).

Buhari ya nemi majalisa ta bashi damar maidawa jihar Borno N16bn

A wani labarin da muka wallafa a baya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nemi amincewar majalisar dattawa don ya maidawa jihar Borno kudi har N16bn.

Kudaden dai a cewar shugaba Buhari na ayyukan titi ne da gwamnanatin jihar Borno ta gudanar, wadanda ya kamata ace gwamnatin tarayya ce ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng