Yadda Muka Rasa ’Yan Uwanmu a Harin ’Yan Bindiga, Mutane Sun Koka a Jihar Plateau
- Wasu da suka tsira daga harin ‘yan bindiga a jihar Plateau sun bayyana irin bala’in da suka gani
- Shugaban kungiyar ci gaban Mwaghavul ya bayyana adadin mutanen da suka rasa rayukansu
- Daga cikin wadanda harin ya rutsa da su akwai wani Rabaran Jesse Jwanle na majami’ar kauyen
Jihar Plateau - Wasu daga cikin wadanda suka tsira daga mummunan harin ‘yan bindiga a jihar Plateau sun bayyana yadda suka dimauce sakamakon harin 'yan bindiga a karamar hukumar Mangu ta jihar.
Harin wanda ya afku a ranar Talata 16 ga watan Mayu ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama musamman mata da yara.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa bayan rasa rayuka da dama da ya hada da mata da yara, an kuma yi asarar dukiyoyi sakamakon harin.
Shugaban kungiya a yankin ya magantu
Shugaban Kungiyar Cigaban Mwaghavul, Joseph Gwankat ya bayyana cewa a yanzu haka adadin mutanen da suka rasa rayukamsu sun kai 85.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga cikin wadanda ya tsira a harin akwai wani Fasto, Rabaran Jesse Joshua Jwanle dake kula da majami’a a kauyen Gaude, cewar jaridar Ripples.
Da yake bayanin yadda Allah ya bashi nasarar kubuta, ya ce “yan bindigan sun kawo hari a kauyen kungiya-kungiya.”
A cewarsa:
“Suna zuwa suka fara kona gidaje, sun kona min gida na nima, dukkan abinda na mallaka na rasa a gidan sai dai kayan da ke jikina yanzu.
“Sun kuma kona dukkan majami’unmu biyu dake kauyen nan, sannan mun rasa daya daga cikin mambobin majami’armu, na gudu zuwa kauyen Halle na dan wani lokaci kafin mu dawo.”
Deborah Samuel, daya daga cikin wadanda suka tsira daga harin daga kauyen Kantoma ta ce ta rasa surkinta da wasu ‘yan uwanta a dalilin harin.
Deborah ta bayyana yadda ta dimauce dalilin harin:
“Abin ba sauki, muna kasuwa kawai sai muka fara jin karan bindiga ta ko wane bangare, sai muka fara gudu, na rasa surki na da wasu kannen mijina su hudu, har yanzu a dimauce nake akan abin da ya faru.”
'Yan Bindiga Sun Sheke Mutum Fiye da 30 a Wani Hari a Jihar Plateau
A wani labarin, yan bindiga sun hallaka mutane fiye da 30 a wani hari a kauyen Tanknale a karamar hukumar Mangu a jihar Plateau.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ne ya tabbatar da haka a ranar Talata 16 ga watan Mayu.
Asali: Legit.ng