An Kuma: An Tasa Keyar Wata Mata Zuwa Gidan Kaso Bayan Ta Ci Zarafin Dan Sanda a Lagos

An Kuma: An Tasa Keyar Wata Mata Zuwa Gidan Kaso Bayan Ta Ci Zarafin Dan Sanda a Lagos

  • Wata mata mai suna Olufunmilayo Brioluwa ta gurfana a gaban kotu bayan ta ci zarafin dan sanda
  • Kakakin rundunar a jihar Lagos, Benjamin ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata 16 ga watan Mayu
  • Hundeyin ya tabbatar da cewa matar ta cacumi wuyar rigar dan sandan ne lokacin da yake bakin aiki

Jihar Lagos - An tasa keyar wata mata mai suna Olufunmilayo Brioluwa zuwa gidan kaso bayan ta ci zarafin jami’in dan sanda a jihar Lagos.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a ranar Talata 16 ga watan Mayu.

dan sanda/mata
Wata Mata Ta Ci Zarafin Dan Sanda a Lagos. Hoto: Tribune
Asali: Facebook

Hundeyin ya ce Brioluwa ta ci zarafin dan sandan ne a yankin Oyingbo na jihar Lagos lokacin da yake binciken ababan hawa don samar da tsaro a yankin.

Yadda matar ta ci zarafin dan sandan

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa Yana Landan, Osinbajo Ya Amince a Kafa Sababbin Jami’o’i 36 a Najeriya

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa matar ta cacumi wuyar rigar dan sandan ne yayin da take masa barazana da nuna isa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tuni aka gurfanar da ita a gaban kotun magistare dake zamanta a karamar hukumar Eti-Osa dake cikin jihar Lagos.

An gurfanar da wadda ake karar ne a gaban mai shari’a Alao M. O. yayin da ta musanta zargin da ake tuhumarta akai.

Hukuncin kotu bayan sauraran kara

Mai shari’an ya ba da umarnin a ci gaba da tsare ta a gidan kaso har tsawon kwanaki 21 kafin kammala bincike.

Za a ci gaba da tsare ta a gidan gyaran hali na Kirkiri har zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraren karar a ranar 6 ga watan Yuni na wannan shekarar.

Wannan hukunci na zuwa ne sa’o’i kadan bayan shahararren mawaki Seun Kuti ya ci zarafin jami’in dan sanda a bakin aiki a jihar.

Kara karanta wannan

Rundunar ’Yan Sanda Ta Bayyana Dalilin da Yasa Suka Sanya Wa Seun Kuti Ankwa Bayan Ya Mika Kansa

Yan Sanda Sun Bayyana Dalilin da Yasa Ta Sanya wa Seun Kuti Ankwa

A wani labarin, jami'an 'yan sandan jihar Lagos sun bayyana dalilinsu na saka wa shahararren mawakin nan Seun kuti ankwa bayan ya mika kansa ga hukumar.

Rundunar ta ce sun saka wa Kuti wanda 'da ne ga tsohon mawaki Feka Kuti saboda doka ta basu daman haka ga duk wani bata gari a cikin al'umma, an kama shi bisa zargin cin zarafin dan sanda a bakin aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.