Aisha Buhari Ta Bayyana Abinda Za a Riƙa Tuna Mijinta Da Shi Bayan Ya Bar Mulki
- Aisha Buhari ta bayyana cewa mijinta Shugaba Muhammadu Buhari, ya bai wa hidimar matasan ƙasar nan muhimmanci sosai
- Ta bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wani shirin kiwon lafiya da matasa masu yi wa ƙasa hidima suka ƙaddamar a Abuja
- Ta buƙaci matasan su ci-gaba da yin aiki tuƙuru wajen ganin an ci-gaba da samun wanzuwar haɗin kai a ƙasar nan
Abuja - Uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari ta ce za a riƙa tuna mijinta Shugaba Buhari a matsayin shugaban ƙasan da ya bai wa matasa muhimmanci.
Ta bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da wani shirin tallafin lafiya ga mutanen karkara (HIRD), na hukumar matasa masu yi wa ƙasa hidima, NYSC, a Abuja, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Buhari na ƙaunar shirin NYSC
Ta ƙara da cewa shugaba Buhari mutum ne da ke matuƙar son shirin na masu yi wa ƙasa hidima wato NYSC, saboda yadda ya ke son ganin haɗin kan 'yan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ƙara da cewar saboda da ƙaunarsu da Buhari ya ke yi, sukan gayyaci matasan masu yi wa ƙasa hidima zuwa gidansu da ke Daura a duk lokacin bukukuwan sallah.
Aisha Buhari ta yi kira ga masu gudanar da shirin da kada su yi ƙasa a gwuiwa wajen tabbatuwar haɗin kan 'yan ƙasa ta hanyar hidimtawa al’umma ba tare da la’akari da jiha ko wurin aiki ba.
Ta kuma ce shirin na HIRD ya ƙayatar da ita sosai, a dalilin haka ne ma ofishinta ya bayar da gudummawar kayan aikin asibitin tafi da gidanka don haɓɓaka nasarar shirin.
Ta ƙara da cewa shirin ya yi matuƙar tasiri musamman ma a yankuna na karkara, wanda a dalilin hakan ne shirin ke ci-gaba da samun yabo daga ciki da wajen ƙasar nan.
Sama da 'yan Najeriya miliyan uku aka taimakawa a cikin shirin - Ahmed
A nasa bangaren, Darakta Janar na hukumar masu yi wa ƙasa hidima, NYSC, Birgediya Janar Yushau Dogara Ahmed ya ce an ƙirƙiro shirin na HIRD ne a 2014 saboda taimakawa marasa ƙarfi da ke a yankunan karkara.
Ya ce shirin ya ƙunshi 'yan bautar ƙasa da suka haɗa da likitoci, masu bada magunguna, ma’aikatan jinya, likitocin haƙori da sauransu, waɗanda suke duba marasa lafiya a kyauta.
The Guardian ta ruwaito Ahmed ya na faɗin cewa kawo yanzu sama da ‘yan Najeriya miliyan uku ne suka ci gajiyar shirin.
Gwamnatin Buhari ta kammala aikin samar da wutar Zungeru
A wani labarin da muka wallafa a baya, kun ji cewa gwamnatin shugaba Buhari ta kammala aikin samar da wutar Zungeru mai ƙarfin megawat 700.
Aikin dai na cikin ayyukan da shugaba Buhari ya yi alƙawarin aiwatarwa a wa'adin mulkinsa.
Asali: Legit.ng