Gwamnan Filato Ya Sanya Dokar Zaman Gida a Karamar Hukuma 1 Tal

Gwamnan Filato Ya Sanya Dokar Zaman Gida a Karamar Hukuma 1 Tal

  • Gwamnati ta sanya dokar zaman gida tsawon awanni 24 a ƙaramar hukumar Mangu ta jihar Filato
  • Wannan ya biyo bayan kisan sama da mutum 20 da wasu mahara suka yi a garuruwan Fungzai da Kubat
  • Rundunar 'yan sanda ta kara girke dakaru a yankin domin dakile abinda ka iya zuwa ya dawo

Plateau - Sama da mutane 20 aka tabbatar da sun mutu zuwa yanzu a ƙauyukan Fungzai da Kubat, ƙaramar hukumar Mangu da ke jihar Filato, Arewa ta Tsakiya.

Wasu majiyoyi daga ƙauyukan sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wasu yan bindiga sun kai mummunan hari Kubat da safiyar ranar Talata, suka banka wa gidaje wuta.

Taswirar jihar Filato.
Gwamnan Filato Ya Sanya Dokar Zaman Gida a Karamar Hukuma 1 Tal Hoto: channelstv
Asali: UGC

Channels tv ta ce maharan ba su tsaya iya nan ba, sai da suka bi dandazon jama'an da suka yi yunkurin barin garin don tsira da rayuwarsu, suka kashe wasu, suka raunata da dama.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kan Mutane a Arewa, Gwamnan APC Ya Fusata Ya Ɗau Mataki

Ganin abinda ya faru a Ƙauyen Kubat da ke maƙotaka da su, mazauna kauyen Fungzai suka tara iyalansu mata da kananan yara da nufin su bar garin don tsira daga mugun nufin yan ta'addan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bisa rashin sa'a motocin da suka ɗauko masu kokarin guduwa da babura suka faɗa tarkon maharan, nan take suka kashe mutum 20, mafi yawa mata da kananan yara.

Gwamnati ta ƙaƙaba dokar zaman gida

Domin dakile yuwuwar ɗaukar fansa da kuma yaɗuwar mummunan lamarin, gwamnati ta ƙaƙaba dokar zaman gida tsawon awanni 24 a ƙaramar hukumar Mangu.

A wata sanarwa da shugaban ƙaramar hukumar, Minister Daput, ya fitar, ya ce sun cimma matsayar sanya dokar zaman gida domin guje shiga yanayin da abun zai fi karfin kowa duba da yawan mutanen da suka mutu.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Filato, DSP Alfred Alabo, ya ce tuni suka kara tura dakaru zuwa kauyukan yayin da suka matsa kaimi don binciko musabbabin wannan harin, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sabon Tsari: FG Ta Kafa Muhimman Sharudda 3 Kafin Kwaso Ragowar Yan Najeriya Daga Sudan

Yan Bindiga Sun Saba Saiti, Sun Bindige Abokin Aikinsu a Kano

A wani labarin kuma Wasu Yan bindiga sun yi yunkurin sace magidanci da ɗansa a jihar Kano, ɗaya daga cikinsu ya mutu.

Rahoton yan sanda ya nuna cewa maharan sun shiga hannu, sun bayyana wanda ya umarci su ɗauke mutumin da ɗansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262