Ba Sabon Abu Bane: Na Sha Kaftawa ’Yan Sanda Mari, Inji Mawakin da Ya Ci Zarafin Jami’i a Bakin Aiki

Ba Sabon Abu Bane: Na Sha Kaftawa ’Yan Sanda Mari, Inji Mawakin da Ya Ci Zarafin Jami’i a Bakin Aiki

  • A wani faifan bidiyon da ya yadu, an gano yadda wani mawaki Seun Kuti yake alfahari akan marin dan sanda
  • Mawakin ya ce ya mari ‘yan sanda da dama wannan ba shi ne na farko ba, ya ce dan sandan ya yi masa barazana
  • Sannan mawakin ya ce yana maraba da bincike inda ya roki sifetan ‘yan sanda ya hukunta duk mai laifi

Jihar Lagos - Wani faifan bidiyon da ya yadu, an gano mawaki Seun Kuti yana alfahari akan marin da ya yiwa dan sanda a bakin aiki.

Duk da yake ba a tabbatar da yaushe aka nadi faifan bidiyon ba, an gano Seun din yana cewa ya mari ‘yan sanda da dama saboda yasan shi waye ne.

Mawaki Seun Kuti/ Yan sanda
Ba Sabon Abu Bane: Na Sha Kaftawa ’Yan Sanda Mari, Inji Mawakin da Ya Ci Zarafin Jami’i a Bakin Aiki, Hoto: Daily Post
Asali: Facebook

A cewarsa:

“Wasu ‘yan sanda za su mare ku, ku zo shafin Instagram kuna bayani, kun san ‘yan sanda nawa na zabgawa mari?.

Kara karanta wannan

Kaico: Matashi Ya Aika Mahaifiyarsa Kiyama Saboda Sabanin da Suka Samu a Kan ₦10,000

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Sun ce saboda ni dan Fela Kuti ne, ba ku sani ba cewa Yesu dan Allah ne shi yasa ya mutu saboda ku? Dole kasan kai waye ne kafin kayi irin haka, don haka nayi haka ne saboda nasan ni waye ne...,”

Jaridar Daily Trust ta tattaro yadda sifetan ‘yan sanda, IGP Usman Alkali Baba ya ba da umarnin kama Kuti bayan an gano shi yana cin zarafin jami’in dan sanda a bakin aiki.

Meye ya hada shi da dan sandan?

Da yake maida martani akan lamarin ta shafin Instagram, mawakin ya tabbatar da cewa dan sandan ya yi yunkurin hallaka shi da iyalansa.

Ya kuma kara da cewa dan sandan ya nemi gafararsa kuma ya yafe masa.

A kalamansa:

“Dan sandan ya yi yunkurin kashe ni da iyalai na, ina da hujjoji amma bazan bayyana ba, ya nemi gafara kuma na yafe masa kuma na amince ba zan dauki mataki ba, kowa ya kama harkokinsa ka da dan sandan ya rasa aikinsa.”

Kara karanta wannan

"Ka yi hauka ne?": Tashin hankali yayin da mawaki ya kaftawa dan sandan Najeriya mari

Ina maraba da 'yan sanda su yi bincike

Akan batun kama shi, mawakin ya ce yana maraba da yin bincike da ‘yan sandan zasu yi.

Ya kara da cewa:

“Ina maraba da bincike sannan zan ba da hadin kai dari bisa dari, ina rokon sifetan ‘yan sanda da a hukunta duk mai laifi."

Wannan na zuwa ne makwanni bayan da wani mawaki Habeeb Okikiola da aka fi sani da Portable aka kama shi kan cin zarafin wasu jami’an ‘yan sanda, cewar jaridar Vanguard.

Yan Bindiga Sun Budewa Yan Sanda 5 Wuta Yayin Da Suke Tsakar Cin Abinci a Imo

A wani labarin, 'Yan bindiga sun bude wa wasu 'yan sanda wuta a yayin da suke cin abinci a ranar idi a jihar Imo.

'Yan bindigan kuma sun kashe wasu ma'aurata a yankin, in da suka wasu mutane da dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.