Shawarin Fasto Ga Obi a Gaba: Ka Waiwayi Matakanka, Ka Hada Kai da Fastoci da Jiga-Jigan Kirista

Shawarin Fasto Ga Obi a Gaba: Ka Waiwayi Matakanka, Ka Hada Kai da Fastoci da Jiga-Jigan Kirista

  • Ikechukwu Samuel, babban limamin cocin Shiloh Word Chapel da ke Abuja ya shawarci Peter Obi da ya koma ga matakansa da ya biyo a sakamakon zaben 2023
  • A sanarwar da ya fitar, ya buga misali da yadda Israilawa suka zabi Saul a matsayin sarki a madadin zabin da Allah ya yi musu na Annabi Isma’il, kamar yadda yazo a Injila
  • Malamin ya ce ya yi mamakin yadda Obi da ya yi takara a jam’iyyar Labour yake mamakin yadda yake fama da kwace hakkinsa a madadin ya waiwaya baya

FCT, AbujaMalamin coci, Ikechukwu Samuel na Shiloh Word Chapel da ke Abuja ya yi tsokaci game da zaben shugaban kasa na 2023 da yadda Bola Ahmad Tinubu ya yi nasara.

A cikin sanarwar da ya fitar, ya bayyana cewa, ya kamata dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Peter Obi ya koma ga matakansa na baya da yadda ya yi takara, rahoton PM News.

Kara karanta wannan

Ya Ci Kamu: Fasto Ya Jawo Cece-Kuce Bayan Bayyana Kiyayyarsa Ga Bola Tinubu

Samuel ya ce, ya yi mamakin yadda Obi ke ta faman cewa sai ya karbi hakkinsa a madadin ya koma baya ya duba matakan da ya biyo tun farko a fafutukarsa ta gaje Buhari.

Obi Allah ya zaba, amma 'yan Najeriya suka so wani
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar Labour | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Shawarin da ya ba Peter Obi game da zaben 2023

A kalamansa, ya shawarci Peter Obi da ya yi duba ga dukkan Annabawan Allah, malamai da makusantan Allah da abubuwan da suka faru dasu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewarsa, dukkan makusanta ubangiji suna da wani aiki na musamman da suke dauke dashi sabanin abin da mutane ke gani, rahoton Vanguard.

Wani yankin sanarwar na cewa:

“Komai girmanka a aikin Allah kana da iyaka, amma tsoka na iya ganin komai da idon siyasa, Ubangiji ya zabi Annabi Isma’il a matsayin sarki amma Isra’ilawa suka zabi Saul, ina da yakinin irin abin da ya faru kenan a Najeriya a yau.

Kara karanta wannan

Har Yanzu Tinubu Bai da ‘Dan Takara a Zaben Shugabannin Majalisa – Zababben Sanata

“Ina ba Peter Obi kwarin gwiwar ya daidaita da dukkan malaman addinin Kirista da fastoci a Najeriya, duk wanda ya shawarce shi da ya ki bin ta malaman coci to shi ya kada shi.”

Sai baka nan za a yi kewarka, ga misalin T.B Joshua, inji fasto

Malamin ya kuma bayyana yadda fasyyo T.B Joshua ya sha fama da mutane a lokacin da yake raye, amma ya samu karbuwa bayan mutuwarsa.

A tun farko, Peter Obi da dan takarar shugaban na PDP, Atiku Abubakar basu amince cewa Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben da aka yi a bana ba.

Sun dunguma kotu domin kwace hakkinsu, wanda tuni aka fara zama don jin yadda zaben ya gudana da kuma yanke hukunci a gaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.