Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Hatsarin Mota a Jihar Bauchi
- Hukumar Kula da Kiyaye Hadura ta Kasa ta tabbatar da faruwar wani mummunan hatsari a hanyar Darazo
- Sanarwar ta ce akalla mutane takwas ne suka mutu yayin wannan hatsari wanda ya hada da mata da yara kanana
- Rahoton ya bayyana hatsarin ya faru ne a kauyen Kili a kan haryar Darazo a ranar Alhamis 11 ga watan Mayu
Jihar Bauchi - Akalla mutane takwas ne suka mutu wasu suka jikkata a wani mummunan hatsarin mota da ta afku a hanyar Darazo dake jihar Bauchi.
Hukumar Kula da Kiyaye Hadura ta kasa FRSC ce ta tabbatar da wannan labari ta bakin Kwamandan hukumar, Yusuf Abdullahi inda ya ce hatsarin ya rutsa da wata mota kirar Sharon mai lamba BCH 456 XA ta kungiyar direbobi da ake amfani da ita don zirga-zirgan fasinjoji.
Rahoton jaridar Punch ta bayyana cewa hatsarin ya faru ne a kauyen Kili a kan haryar Darazo a ranar Alhamis 11 ga watan Mayu da misalin karfe 12:03 na rana.
Masu ba da agajin gaggawa sun halarci wurin da gaggawa don ceto wadanda suka jikkata da misalin karfe 12:10 na rana.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Mutanen da suka tsinci kansu a hatsarin sun kai 15 wadanda suka hada da mata 4 da maza 6 da kuma yara maza 2 da mata 3.” In ji sanarwar.
Da yake bayyana yawan wadanda suka jikkata, kwamandan ya ce mata hudu ne suka jikkata da namiji daya da kuma yara biyu mata.
Har ila yau, irin raunukan da mutanen suka samu sun hada da kujewa, buguwan kai, da karaya musabbabin hatsarin kuma an tabbatar da cewa fashewar taya ce ta jawo,
Mutane 8 sun mutu a hatsarin
Takwas da suka rasa rayukansu a hatsarin sun hada da maza uku da mata biyu da yara maza guda biyu sai yarinya mace guda daya.
An kwashi gawarwakin da kuma wadanda suka ji ciwo zuwa babban asibitin Darazo don tabbatar mutuwarsu da kuma bai wa masu raunuka kulawan gaggawa.
Mummunan Hatsari Mota Ya Rutsa da Daliban Jami'a a Jihar Bayelsa
A wani labarin, akalla mutane 5 suka mutu lokacin da wani mummunan hatsari ya afku a kan titin Amossam-Tombia dake jihar Bayelsa.
Hatsarin ya rutsa da Motar Mazda mai ɗauke da kusan mutum 7 ciki har da ɗaliban jami'ar Neja Delta (NDU).
Asali: Legit.ng