FG Ta Karɓi 'Yan Najeriya 147 Da Suka Maƙale a Jamhuriyar Nijar
- 'Yan Najeriya, 147 'yan ci rani da suka maƙale a jamhuriyar Nijar ne aka samu nasarar dawowa da su gida lami lafiya
- Hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, ce ta tarbi masu dawowar a filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano
- An shawarci matasa da su riƙa ƙoƙarin neman damammaki a gida Najeriya ba wai dole sai sun tafi zuwa wata ƙasar ba
Jihar Kano - A jiya Laraba ne gwamnatin tarayya ta karɓi ƙarin wasu 'yan Najeriya 147 daga Yamai, babban birnin jamhuriyar Nijar.
Mutanen, waɗanda suka iso filin tashi da saukar jirage na Malam Aminu Kano ranar Laraba, sun haɗa da maza manya 77 da yara 16, mata manya 23 da yara 21 daga jihohi daban-daban ciki hadda Legas, Kano, Katsina, Jigawa da Kaduna kamar yadda Vanguard ta yi rahoto.

Kara karanta wannan
Ziyarar Tinubu Zuwa Rivers: An Zargi Wike Da Tinubu Da Shirya Wata Maƙarƙashiya Kan Atiku

Source: UGC
Wata kungiya ce ta taimaka wajen dawowa da su
Hukumar ba da agajin gaggawa NEMA, ta bayyana cewa an samu nasarar dawo da mutanen ne ƙarƙashin wani shiri na wata ƙungiyar sa kai da ke kula da masu gudun hijira wato IOM.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An ƙirƙiro shirin ne musamman domin kula da 'yan Najeriya, da kan tafi ci rani zuwa wata ƙasar amma daga bisani su gaza dawowa gida.
Shugaban hukumar NEMA reshen jihar Kano, Nuraddeen Abdullahi, ya shaidawa manema labarai cewa za a bai wa mutanen da aka dawo da su horo na musamman, kan yadda za su tsayu da ƙafafuwansu sannan kuma a basu jari da za su fara sana'a da shi.
Haka nan kuma, Abdullahi ya shawarci matasan Najeriya kan cewa su daina jefa kansu cikin haɗari da sunan zuwa ci rani wasu ƙasashen.
An yi kira ga matasa su rika tsayawa suna neman kudinsu a Najeriya
Ya ƙara da cewar gwamma mutum ya nemi hanyoyin neman abinci a cikin gida Najeriya. Idan kuma mutum ya na son dole sai ya fita zuwa wata ƙasar, to ya yi hakan ta hanyar da ta dace domin gudun faɗawa hannun masu safarar mutane da makamantansu.
A nasu ɓangaren, mutanen sun godewa gwamnatin tarayya da kuma IOM, bisa ƙoƙarin da suka yi musu na dawowa gida lafiya.
Wata daga cikin waɗanda aka dawo da su mai suna Ngozi Ogbu ta ce sun ci baƙar wahala a yayin tafiyar da har ya kai ga sun fara fidda rai da rayuwarsu, kafin daga bisani, Ubangiji ya kawo musu ɗauki, a rahoton da Channels TV ta wallafa.
Rikicin Sudan zai jawo karin kudin jigilar mahajjata
A wani labari da muka wallafa a baya, ana ganin cewa rikicin da ke faruwa a kasar Sudan zai jawo karin kudin jirgi ga kowane mahajjaci.
Hakan dai ya biyo bayan korafin da masu kamfanonin jiragen sama suka yi, na cewar yawan mai da za su sha zai karu sakamakon zagaye ma Sudan da za a yi a yayin jigilar.
Asali: Legit.ng
