Majalisar Jihar Sokoto Ta Sanya Dokar Rage Kashe Kuɗin Aure, Suna, Da Kaciya

Majalisar Jihar Sokoto Ta Sanya Dokar Rage Kashe Kuɗin Aure, Suna, Da Kaciya

  • 'Yan majalisar dokokin jihar Sokoto sun yi dokar da za ta rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa a wajen bukukuwan aure da sauran bukukuwan gargajiya
  • Sun ce sun yi hakan ne domin rage tsadar aure da bikin suna, da na kaciya wanda hakan kan janyo ƙarin wahalhalu ga masu yin hidindimun
  • Kaso mafi rinjaye na 'yan majalisar sun amince da sabon ƙudirin dokar da aka kawo ta taƙaita almubazzaranci a bukukuwa

Sokoto - A ranar Talata ne dai majalisar jihar Sokoto ta yi wata sabuwar doka ta rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa a wajen bukukuwan aure a jihar.

Ɗan majalisan da ke wakiltar ƙaramar hukumar Yabo, Alhaji Abubakar Shehu na APC da kuma takwaransa da ke wakiltar ƙaramar hukumar Gudu, Faruk Balle na PDP ne suka gabatar da ƙudurin a gaban majalisar Daily Trust tai rahoto.

Kara karanta wannan

Mutane 8 Sun Riga Mu Gidan Gaskiya a Haɗarin Kwale-kwale a Zamfara

Majalisar Jihar Sokoto
Majalisar Jihar Sokoto. Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Kuɗurin ya samu karɓuwa a majalisar

Abubakar Shehu wanda ya kasance shine shugaban kwamitin Addini na majalisar, ya gabatar da ƙudurin wanda kuma ya samu karɓuwa da kaso mafi rinjaye na majalisar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙudurin dai ya buƙaci a rage yawan almubazzarantar da kuɗaɗen da ake yi a yayin bukukuwan aure, suna, kaciya da kuma wasu sauran bukukuwa na al'ada da akan gudanar a jihar.

A yayin da ya ke gabatar da ƙudurin, Shehu ya ce kwamitin na su ya yi zama da masu ruwa da tsaki, waɗanda suka bada ƙarin wasu shawarwarin da suke a ƙunshe cikin ƙudurin.

Bayan tattaunawa tsakanin 'yan majalisun a zaman da mataimakin kakakin majalissar ta Sokoto Alhaji Abubakar Magaji ya jagoranta, 'yan majalissun sun amince da tabbatar da ƙudurin.

Wani daga cikin 'yan majalissun da BBC Hausa ta zanta da shi, ya bayyana cewa an tanaji hukunci ga duk wanda aka samu ya karyar dokar rage kashe kudade a hidindimun auren.

Kara karanta wannan

Kotun Ƙarar Zaɓe: Atiku Ya Buƙaci A Haska Zaman Kotun Kai Tsaye A Talabijin

An kama wata mata da ta siyar da jaririnta

A wani labari da muka wallafa a kwanakin baya, kunji yadda 'yan sanda suka kama wata mata a jihar Ogun kan laifin siyar da jaririnta da ta yi akan kudi N600,000.

Mijin matar ne ya kai kararta wajen jam'ian 'yan sanda, wadanda su kuma suka cafke ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng