Yanzu-Yanzu: Wasu Karin Yan Najeriya Da Suka Makale a Sudan Sun Iso Gida
- Wasu daga cikin ƴan Najeriyar da ake kwasowa daga rikicin dan sun iso gida Najeriya daga biranen Aswan da Port Sudan
- Jiragen sama guda uku ne dai suka sauka a birnin tarayya Abuja ɗauke da mutanen
- Jiragen saman Azman Air da Max Air sun taso ne daga birnin Aswan na Egypt, yayin da jirgin Tarco Airlines ya taso daga Port Sudan
Abuja - Wasu ƙarin ƴan Najeriyan da suka maƙale a rikicin Sudan, sun iso gida Najeriya a ranar Lahadi.
Jaridar Punch ta kawo rahoto cewa, mutum ɗari takwas da talatin da shida ne, suka iso birnin tarayya Abuja, daga ƙasar Masar.

Source: Twitter
An ɗauko su ne a jiragen sama na kamfanunnikan Max Air, Azman da Tarco Airlines.
Jiragen sama na Max Air da Azman Air sun iso ɗauke da mutum 410 da 324, waɗanda aka kwaso daga birnin Aswan na ƙasar Masar.

Kara karanta wannan
Sarki Charles III: Zafafan Hotuna 7 Yayin Da Aka Nada Sabon Sarkin Ingila Tare Da Matarsa
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tarco Airlines ya taho da ƴan Najeriya 102 da Port Sudan.
Channels Tv tace jirgin Tarco ya taso ne daga tashar tashi da sauka ta jiirgin sama a Port Sudan da misalin ƙarfe 5:25 na safiyar ranar Lahadi, sannan ya iso tashar jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, da misalin ƙarfe 12:40 na rana.
Wannan rukunin da suka iso gida Najeriya, shi ne rukuni na huɗu na ƴan Najeriyan da aka kwaso daga rikicin Sudan.
Jiragen saman Max Air da Azman Air da suka taso daga birnin Aswan, su ne suka taho da ƴan Najeriya na ƙarshe da za a kwaso daga birnin na Aswan na ƙasar Masar.
A yanzu kwaso ragowar sauran ƴan Najeriyan, zai koma ne kacokan a birnin Port Sudan.
Gwamnatin tarayya ta dai ƙara zage damtse domin ganin ta kwaso ƴan Najeriyan da rikicin na Sudan ya ritsa da su.
Hajiya Turai Ta Bayyana Abinda Mijinta Ya So Yi a Rayuwa

Kara karanta wannan
Tashin Hankalin Da Muka Shiga a Sudan Ba Ɗan Kaɗan Ba Ne, In Ji Ɗalibi Bello Halliru
A wani rahoton na daban kuma, uwargidan tsohon shugaban ƙasa, marigayi Umaru Musa Yar'adua, Hajiya Turai, ta bayyana abinda tsohon shugaban ƙasar ya so ya yi a rayuwa.
Hajiya Turai tace marigayin bai taɓa son ya shiga harkar siyasa ballantana har ya yi shugaban ƙasar Najeriya.
Asali: Legit.ng