Badakalar N2.1bn: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Daurin Shekaru 8 Da Aka Yi Wa Maina

Badakalar N2.1bn: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Daurin Shekaru 8 Da Aka Yi Wa Maina

  • Kotun daukaka kara ta kori karar da Abdulrasheed Maina ya daukaka kan daurin da aka yi masa
  • Tun farko tsohon shugaban hukumar na fansho ya daukaka kara kan zargin rashin ba shi damar kare kansa daga zargin da hukumar EFCC ta gurfanar da shi a kai
  • An dai yankewa Maina hukuncin daurin shekaru takwas a gidan gyara hali kan karkatar da Naira biliyan 2.1 na ’yan fansho

Abuja - Kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da hukunci da daurin shekaru takwas da aka yi wa tsohon shugaban hukumar fansho, Abdulrasheed Maina kan wawure kimanin naira biliyan 2.1.

Kwamitin mutum uku na kotun ta tabbatar da hukuncin da Justis Okon Abang na babbar kotun tarayya, Abuja ya zartar a ranar 8 ga watan Nuwamban 2021.

Abdulrasheed Maina
Badakalar N2.1bn: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Daurin Shekaru 8 Da Aka Yi Wa Maina Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

A cikin hukuncin da Justis Elfreda Williams-Daudu ta yanke, ta kuma tabbatar da hukunci mabanbanta da aka zartar a yayin shari’ar a babbar kotun tarayya, wanda Maina ya daukaka kara.

Kara karanta wannan

Ekweremadu: Abu 5 Game Da Tsohon Mataimakin Majalisar Dattawar Najeriya Da Aka Yanke Wa Shekara 10 a Birtaniya

Yayin da take warware lamuran biyu, Justis Williams-Daudu, ta riki cewa kotun ta ba shi damar kare kansa daga zargin, amma ya ki yi har lokaci ya kure, sannan ya gaza kawo kwararan hujjojin da za su wanke shi daga laifin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun ta ce za a fara lissafin shekara takwas din ne daga lokacin da aka fara tsare shi a shekarar 2019, rahoton Aminiya.

An dai gurfanar da Maina a ranar 25 ga watan Oktoban 2019 kan tuhume-tuhume 12 sannan aka kuma gurfanar da dansa, Faisal, kan tuhume-tuhume uku da suka hada da wawure kudi da kuma boye wasu kudaden haram.

Zan yi koyi da Marigayi Umaru Musa Yar'adu, Tinubu

A wani labari na daban, zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya jinjinawa marigayi tsohon shugaban kasa Umaru Musa Yar'adua kan tabbatar da damokradiyya da ya yi a kasar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Birtaniya Ta Yanke Wa Ekweremadu Shekaru 10 A Gidan Yari Kan Safarar Sassan Jikin Bil Adama

Tinubu wanda ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai son ci gaba da zaman lafiya ya sha alwashin koyi da tsohon shugaban kasar idan ya karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

A ranar Juma'a, 5 ga watan Mayun 2023 ne Yar'adu ya cika shekaru 13 da rasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng