Shekaru 13 Da Rasuwa: Tinubu Ya Jinjinawa Marigayi Yar'Adua, Ya Ce Zai Yi Koyi Da Shi

Shekaru 13 Da Rasuwa: Tinubu Ya Jinjinawa Marigayi Yar'Adua, Ya Ce Zai Yi Koyi Da Shi

  • Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya tuna da rasuwar marigayi Shugaban kasa Umaru Musa Yar'Adua
  • Tinubu, a sakon cika shekaru 13 da rasuwar marigayi Yar'adua, ya bayyana shi ba matsayin mutum mai gaskiya da jajircewa
  • Tsohon gwamnan na jihar Lagas ya sha alwashin yin koyi da marigayi shugaban kasar idan ya karbi ragamar shugabanci a ranar 29 ga watan Mayu

Zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu ya jinjinawa marigayi Shugaban kasa Umar Musa Yar’Adua kan jajircewarsa da damokradiyya da shugabanci nagari.

Tinubu wanda ya yi jinjinar a ranar Juma’a, 5 ga watan Mayu, ya yi alkawarin koyi ga marigayi Shugaban kasar, rahoton Vanguard.

Bola Tinubu da Umaru Musa Yar'adua
Shekaru 13 Da Rasuwa: Tinubu Ya Tuna Da Marigayi Yar'Adua Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Jim Watson/AFP
Asali: UGC

A jawabin tunawa da ranar mutuwarsa dauke da sa hannun Tinubu, zababben shugaban kasar ya ce marigayi Yar’Adua ya yi rayuwa mai ma’ana.

Kara karanta wannan

Jiga-Jigan PDP Da Al'ummar Katsina Sun Yi Taron Addu'a Don Tunawa Da Marigayi Yar'adua

Jaridar The Nation ta nakalto Tinubu yana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ba za mu taba mantawa da kai ba! A yau, kamar kullun, na tuna da abokina nagari kuma dan uwa a fafutukar tabbatar da damokradiya da shugabanci mai kyau a Najeriya, Marigayi Shugaban kasa Umaru Musa Yar’Adua, wanda ya rasu a rana irin ta yau shekaru 13 da suka shige.
“Ranar 5 ga watan Mayun 2010 ta wuce amma ga wasunmu, har yanzu ciwon na nan sabo. Muna tunawa da ranar Kamar yadda muke tunawa da rayuwa mai ma’ana da Yar’Adua ya yi.
“A matsayinsa na aboki kuma hadimi a siyasa ina mutunta abubuwan da suka faru na gaskiya, dagewa, kishin kasa da kuma nagartattun abubuwan da Marigayi ‘Yar’Adua ya bari a matsayin gwamnan Katsina (1999 zuwa 2007) da kuma shugaban Najeriya (2007 zuwa 2010).

Kara karanta wannan

Shekara 13: Yadda Katsinawa da Jiga-Jigan PDP Suka Roki Allah Ya Gafarta Wa Umaru Musa Yar'Adua

“Yayin da nake shirin karbar ragamar mulkin kasar a ranar 29 ga watan Mayu, na kuduri aniyar yin koyi da kyawawan misalai da shugabanni irin su Malam Umaru Yar’adua suka bari wadanda suka nuna nagarta ta kwarai da kuma sadaukar da kai ga kasarmu mai albarka.
“Ka ci gaba da hutawa dan uwa. Allah ya kanka yayin da kake tare da mahaliccinka, amin.”

Katsinawa da yan PDP sun yi addu'ar tunawa da Yar'adua

A gefe guda, mun kawo a baya cewa mazauna jihar Katsina da jam'iyyar PDP sun gudanar da taron addu'a na musamman ga marigayi Umaru Musa Yar'adua yayin da ya cika shekaru 13 da rasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: