Yanzu Yanzu: Jirgin Shugaban Kasa Ya Tashi Zuwa Kasar Waje Don Samun Gyara Mai Kyau
Gabannin bikin rantsar da sabon shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu, jirgin shugaban kasar Najeriya kirar Boeing 737 ya tashi zuwa wajen kasar domin samun gyara mai kyau, jaridar Punch ta rahoto.
Majiyoyin fadar shugaban kasa sun bayyanawa manema labarai cewa an fitar da jirgin NAF 001, wanda ya yi jigilar shugaban kasa Muhammadu Buhari tsawon shekaru takwas da suka gabata daga kasar a karshen makon nan.
Koda dai ba a san inda jirgin ya je ba, kamfanin Boeing da ke kasar Amurka ne ke kula da jirgin a baya.
Tafiya na karshe da jirgin mai shekaru 20 ya yi shine jigilar shugaban kasa zuwa Accra, babban birnin kasar Ghana, inda ya halarci wani taro.
Majiyar ta ce nan da makonni hudu masu zuwa za a sake jigilar Buhari a wani jirgin saman shugaban kasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A ranar Talata, 3 ga watan Afrilun 2001, majalisar dattawa ta amince da naira biliyan 5.5 don siyawa shugaban kasar wancan lokacin, Olusegun Obasanjo sabon jirgin sama, rahoton The Eagle.
A watan Fabrairun wannan shekarar, Obasanjo ya nemi amincewar majalisa don sakin dala miliyan 19 daga cikin kudaden siyan sabbin jiragen sama takwas a fadar shugaban kasa.
Motocin bas masu amfani da lantarki sun iso Lagas don saukaka sufuri
A wani labarin, mun ji cewa domin saukaka zirga-zirgar jama'a, gwamnatin jihar Lagas ta karbi rukunin farko na motocin bas masu amfani da lantarki.
Gwamna Babajide Sanwo-Olu ne ya sanar da ci gaban a shafinsa na soshiyal midiya yana mai bayyana hakan a matsayin kokarin da gwamnatinsa ke na zamanantar da kowani bangare a jihar.
Ya kuma bayyana cewa idan motar ya samu cikakken chaji yana iya tafiya mai tsawon kilomita 280.
Buhari ya tsawaita wa'adin shugaban hukumar NIS har zuwa karshen mulkinsa
A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara tsawaita wa'adin shugabancin kwanturola Janar na hukumar kula da shige da fice na kasa, Isah Jere Idris har zuwa ranar 29 ga watan Mayu.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban ma'aikatan shugaban kasa Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari.
Asali: Legit.ng