Buhari Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Hukumar NIS Isah Jere

Buhari Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Hukumar NIS Isah Jere

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da tsawaita wa'adin mulkin Isah Jere Idris a matsayin Kwanturola Janar na hukumar NIS
  • Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari
  • Kamar yadda yake a wasikar, Jere ne zai ci gaba da kasancewa a matsayin shugaban NIS har zuwa ranar 29 ga watan Mayu lokacin da wa'adin Shugaba Buhari zai kare

FCT, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar da tsawaita wa'adin shugabancin Isah Jere Idris a matsayin Kwanturola Janar na hukumar shige da fice ta kasa (NIS) har zuwa ranar Litinin, 29 ga watan Mayu.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa wannan ci gaban na kunshe ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun shugaban ma'aikatan shugaban kasa Buhari, Farfesa Ibrahim Gambari.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Karbi Bakuncin Zababben Shugaban Kasa Tinubu, Hotuna Sun Bayyana

Wannan shine karin wa'adi na biyu da Kere ke samu duk da cewar ya rigada ya wuce lokacin ritayarsa a aiki ya wuce.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Buhari Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Hukumar NIS Isah Jere Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

Da yake martani ga wannan ci gaban, kakakin hukumar NIS, Tony Akuneme, ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"CG ya samu sabuwar wasika da ta shafe wacce ta umurce shi da ya bar ofis. An tsawaita wa'adinsa har zuwa karshen wa'adin mulkin shugaban kasar. Wata daya ne kawai."

An tattaro cewa kafin karin wa'adin da aka yi wa Jere a yanzu, an aika wata wasika a ranar Litinin, 17 ga watan Afrilu, inda aka yi umurnin ya bar ofis tare da shugaban hukumar Civiel Defence, hukumar gidan gyara hali da hukumar kwana-kwana a ranar Litinin, 24 ga watan Afrilu kafin a nada sabon kwanturola Janar.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Obasi Edozie Edmund, mukaddashin sakataren hukumar, ya sanya hannu a wasikar.

Kara karanta wannan

Zargin Kisan Kai: Doguwa Ya Shiga Matsala Yayin Da Kotu Ta Ba Atoni Janar Na Jihar Kano Sabon Umurni

Wannan ci gaban ya haifar da rade-radin cewa wasu jami'ai na shirin yin zanga-zanga idan aka Shugaban kasa ya kara wa'adin Jere.

Rahotanni sun ce wasu kungiyoyin jama'a sun gudanar da zanga-zangar a ranar Juma'a, 28 ga watan Afrilu suna neman Jere ya yi murabus daga kujerarsa.

An gudanar da zanga-zangar ne a hedkwatar hukumar NIS da ma'aikatar cikin gida a Abuja don watsi da ci gaba da kasancewar CG din a ofis.

Masu zanga-zangar na korafin cewa ci gaba da kasancewar Jere a ofis baya bisa ka'ida domin ya saba tsarin hukumar shige da fice.

Buhari ya lamuncewa dan takarar gwamnan APC a Kogi

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lamuncewa dan takarar gwamnan APC a jihar Kogi, Usman Ododo domin ya gaji Yahaya Bello.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng