Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Daliban Jami'a a Bayelsa, An Rasa Rayuka

Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Daliban Jami'a a Bayelsa, An Rasa Rayuka

  • Wani mummunan hatsarin mota ya yi ajalin mutane biyar a jihar Bayelsa ranar Jumu'a 28 ga watan Afrilu, 2023
  • Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin motocin da haɗarin ya rutsa da su ta ɗauko ɗaliban jami'ar Neja Delta ta nufi Yenagoa
  • Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Bayelsa, SP Asinim Butswat, ya ce suna fara bincike kan abinda ya haddasa hatsarin

Bayelsa - Mutane 5 sun mutu a wani mummunan haɗarin Mota da ya rutsa da su a kan titin Amassoma-Tombia da ke yankin ƙaramar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa.

Daily Trust ta tattaro cewa haɗarin, wanda ya auku ranar Jumu'a da yamma, ya rutsa da Motar Mazda mai ɗauke da kusan mutum 7 ciki har da ɗaliban jami'ar Neja Delta (NDU).

Taswirar jihar Bayelsa
Mummunan Hatsari Ya Rutsa da Daliban Jami'a a Bayelsa, An Rasa Rayuka Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Motar da ɗaliban ke ciki ta taso ne daga garin Amassoma, kudancin ƙaramar hukumar Ijaw zuwa Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wainna Ilaihir Rajiun: Wata Dalibar Jami'a Ta Fadi Ta Rasu Tana Kammala Jarabawa

Motar ta yi taho mu gama da wata motar toyota SUV baƙa wacce ta nufi garin Amassoma, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fasinjoji 4 da Direban Motar Mazda sun mutu nan take yayin da aka samu nasarar tsamo mutum ɗaya a raye kuma tuni aka nufi Asibitin koyarwa na jami'ar Neja Delta.

Wane kokari yan sanda suka yi?

Har kawo yanzun ba'a san musabbabin da ya haddasa hatsarin ba amma hukumar 'yan sanda a jihar Bayelsa ta ce ta fara bincike don gano abinda ya jawo taho mu gamar motocin.

Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar 'yan sandan jihar, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce tuni suka kai gawarwakin fasinjojin Asibitin koyarwa na jami'a domin bincike.

Ya ce jami'ai na kan gudanar da bincike domin damƙe direban motar SUV da kuma gano asalin abinda ya haddasa mummunan haɗarin.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An Samu Wata Fashewa A Babban Birnin Jihar Arewa, Mutane da Yawa Sun Mutu

Motar Tanka ta fashe a Jos

A wani labarin kuma Kun Ji Cewa Mutum 10 Sun Mutu Yayin da Wata Tanka Ta Fashe a Jihar Filato

Lamarin ya faru ne a lokacin Tankar maƙare da Man Fetur ta kucce wa direba, kana ta fashe kuma ta kama da wuta a Jos, babban birnin jihar.

Zuwa yanzun mutane 10 suka kone ƙurmus yayin da ake ci gaba da aikin tantance yawan mutanen da hatsarin ya rutsa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

iiq_pixel