Muhuyi Rimin Gado: Gwamnatin Ganduje Ta Biya Tsohon Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Hakkokinsa

Muhuyi Rimin Gado: Gwamnatin Ganduje Ta Biya Tsohon Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Hakkokinsa

  • Kotu ta umurci gwamnain jihar Kano ta biya tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da amsar korafe-korafen jama'a ta jihar, Muhuyi Rimin Gado hakkokinsa
  • Tuni gwamnatin Ganduje ya biya Rimin Gado hakkinsa na fiye da miliyan 5 lakadan ba ajalan ba
  • An fara amfani da kudaden wajen siyan magunguna, tukwanen makabartu da taimakon marasa lafiya a asibiti

Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya biya tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafe-korafen jama'a ta jihar, Muhuyi Rimin Gado hakkokinsa na sama da naira miliyan 5 a kotu, jaridar Aminiya ta rahoto.

Tun farko dai Rimin Gado ya shigar da karar gwamnatin Ganduje gaban kotu inda ya nemi a biya shi hakkokinsa bayan tsige shi daga kan kujerarsa ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Abu 3 da Tinubu Zai Bayyana Ranar da Rantsarwa Da Ka Iya Gigita Yan Najeriya

Ganduje ya biya tsohon Shugaban Hukumar Yaki da rashawa na Kano Hakkokinsa
Muhuyi Rimin Gado: Gwamnatin Ganduje Ta Biya Tsohon Shugaban Hukumar Yaki Da Rashawa Hakkokinsa Hoto: Collage/Kano
Asali: Facebook

Bayan nan sai kotun ta umurci gwamnatin Kano ta biya shi hakkokin nasa, da kuma tabbatar da shi a matsayin sahihin shugaban hukumar.

An tattaro cewa tuni Ganduju ya biya Rimin Gado hakkin nasa a hannu kuma har ya fara amfani da su nan take.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ba saboda kudi na yi karar Ganduje ba, Rimin Gado ya yi martani

Sai dai kuma, tsohon shugaban hukumar yaki da cin hancin ya ce ba saboda kudi ya maka gwamnatin Kano a kotu ba, sai domin tabbatar da ganin cewa doka da oda suna aiki a jihar.

Aminiya ta nakalto yana cewa:

"Dama dai ba batun kudin bane matsala ta ba, a'a an amshi kudi ne daga wurin wadanda ba sa son biyan hakki.
"Abubuwan da muke kashe kudin a kansu sune sayen magunguna da tukwanen da za a saya na makabartu da kuma taimakawa marasa lafiya da ke kwance a asibiti."

Kara karanta wannan

Zargin Kisan Kai: Doguwa Ya Shiga Matsala Yayin Da Kotu Ta Ba Atoni Janar Na Jihar Kano Sabon Umurni

Tinubu ya karbi bakuncin gwamnonin PDP 2

A wani labari na daban, mun ji cewa zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da wasu gwamnonin jam'iyyar PDP biyu a gidan gwamnati na 'Defence House', Abuja.

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas da Seyi Makinde na jihar Oyo ne suka kai wa Tinubu ziyarar a ranar Juma'a, 28 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: