“Duk Da Haka Cikakkiyar Matar Gida Zan Zama” – Matashiya Ta Ayyana Yayin da Ta Kammala Jami’a a Bidiyo
- Wata matashiyar budurwa da ta kammala jami'a ta ayyana cewar za ta zama cikakkiyar matar gida duk da cewar ta mallaki digiri
- Ta wallafa wani bidiyo a TikTok wanda ke nuna lokacin da take tafiyar kasaita zuwa wajen bikin yaye daliban
- Cewar da ta yi za ta zama cikakkiyar matar gida ya sa bidiyon ya yadu, inda mutane da dama suka goyi bayanta
Wata matashiya da ta kammala jami'a ta ayyana cewar duk da tana da digiri za ta zama cikakkiyar matar gida ce.
A wani bidiyo da @nano_languza ta wallafa, an gano matashiyar tana tafiyar kasaita zuwa wajen bikin yaye su.
Matashiyar, wacce ta yi shiga ta alfarma a sanye da rigar yaye dalibai a sama da takalmanta masu tsini, ta ce bai kamata mutane su bari kwalin digiri dinta ya yaudaresu.
Wannan bayani da ta yi da kuma ganin cike ta yi shi ne a ranar da ta kammala karatunta ya baiwa mutane da dama mamaki.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A halin da ake ciki, jama'a sun yi martani a kan bidiyon bayan ta wallafa shi a TikTok. Bidiyon ya samu mutane miliyan 1.1 da suka kalle shi.
Yayin da wasu suka yarda da ita, wasu sun ce ya kamata mata masu ilimi su zama masu yanci.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Shortcake ta ce:
"Yadda kike tafiya ba ji ba gani kan wadannan takalman. Ki zamo matar gida kin fi karfin shan wahala."
@Tigiblues ta ce:
"Ki fada da babban murya sahiba, ina da digiri biyu kuma ina son zama matar gida."
@boitumelomotaung34 ta ce:
"Gashin ne ya burge ni."
@55 ta ce:
"Muna samun digirin ne don wuce lokaci."
“Mutuwar Aure 1, ‘Da 1, Yajin Aiki 2”: Matashiya Ta Bayyana Gwagwarmayar Da Ta Sha Kafin Gama Digiri
@Jesus Lover ta yi martani:
"Kwalin digirina na kawata bangon gidanmu ne."
Matar aure ta cika da farin cikin ganin surukarta, ta taka rawa a bidiyo
A wani labarin, wata matar aure ta cika da farin cikin uwar mijinta yayin da ta kawo masu ziyara.
Saboda tsananin farin ciki, harda rawa matar ta taka kuma surukar tata ta tayata takawa. Ta kuma kawo masu sha tara ta arziki kama daga kayan abinci.
Asali: Legit.ng