29 Ga Watan Mayu: Sanar Da Oyetola a Matsayin Shugaban Ma’aikata Da Wasu Abubuwa 2 Da Tinubu Zai Iya Yi

29 Ga Watan Mayu: Sanar Da Oyetola a Matsayin Shugaban Ma’aikata Da Wasu Abubuwa 2 Da Tinubu Zai Iya Yi

Zababben shugaban kasa, Bola Tinubu, zai karbi mulki daga hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a hukumance a ranar 29 ga watan Mayu.

Idan aka yi la'akari da yakin neman zabensa da harkokin siyasarsa a yan kwanakin da suka gabata, zababben shugaban kasar na iya baiwa yan Najeriya mamaki a ranar rantsar da shi da wasu umurni da zai aiwatar.

Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
29 Ga Watan Mayu: Sanar Da Oyetola a Matsayin Shugaban Ma’aikata Da Wasu Abubuwa 2 Da Tinubu Zai Iya Yi Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Ga jerin wasu umurni da zai iya zartarwa a kasa:

1. Cire tallafin mai

Abu guda da Tinubu zai iya fara gwamnatinsa da shi shine cire tallafin man fetur.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kasancewarsa kwararre a bangaren tattalin arziki, zababben shugaban kasar, a lokacin yakin neman zabensa ya sha alwashin cire tallafin mai, duk da tsawon lokacin da yan Najeriya za su dauka suna adawa da haka.

Kara karanta wannan

Somin-tabi: Bidiyon lokacin da Tinubu da Shettima ke kaura zuwa gidan gwamnati

A lokacin da yake nuna adawa ga manufar sauya kudi da ya tabarbarar da tattalin arzikin Najeriya yan makonni kafin zabe, Gwamna Nasir El-Rufai ya ce baya cikin tsarin APC ci gaba da tallafin mai.

Kalli bidiyon a kasa:

2. Ayyana dokar ta baci a bangaren wutar lantarki

Tabbatar da daidaituwar wutar lantarki a Najeriya na daya daga cikin abubuwan da Tinubu ya yi magana sosai a kansu a lokacin yakin neman zabensa, kuma ya yi alkawarin tabbatar da ganin cewa ya farfado da ita.

Saboda haka, zababben shugaban kasar na iya ayyana dokar ta baki a kan wutar lantarko da kuma dakatar da kiyastaccen lissafi.

Kiyastaccen lissafi shine tsarin biyan kudin wuta da kamfanonin DisCos suka dade suna amfani da shi ba tare da mita ba. Wannan kan sa caji kwastamomi kudi da yawa kuma an bayyana hakan a matsayin rashawa.

Da hawansa mulki a 2015, Shugaba Buhari ya yi yunkurin dakatar da kiyastaccem lissafi ta hanyar umurtan dukkanin yan Najeriya da su samu mita. Sai dai mita yan kadan aka bayar, yayin da aka bukaci saura su biya kudi. Abun takaici, wadanda ke da niyan biya basu samu ta sauki ko cikin gaggawa ba.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun tarayya ta yanke hukunci kan karar da Binani ta shigar game da zaben Adamawa

Kalli bidiyon a kasa:

3. Ayyana Oyetola a matsayin shugaban ma'aikata

Wani abun da Tinubu zai iya yi a wajen rantsar da shi shine ayyana shugaban ma'aikatansa da kuma yan nade-nade kadan.

Ana ta rade-radin cewa an tanadarwa kakain majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila ko Babatunde Fashola, minsitan ayyuka da gidaje mukamin shugaban ma'aikata, wanda ya yi aiki a matsayin shugaban ma'aikatan Tinubu lokacin da yake gwamnan jihar Lagas.

Sai dai kuma, Tinubu na iya ayyana Gboyega Oyetola, tsohon gwamnan jihar Osun wanda bai samu zarcewa a karo na biyu ba a matsayin shugaban ma'aikatansa.

Ana hasashen ne duba ga ganin cewa Tinubu da Oyetola yan uwa ne. An ce da mahaifiyar Tinubu da ta Oyetola mahaifinsu daya. Wannan kusanci nasu na iya sa ya ayyana shi a matsayin shugaban ma'aikatansa bayan rantsar da shi.

MURIC ta bukaci hukumomin tsaro su kara ba Tinubu da Shettima kariya

A wani labarin, mun ji cewa kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta bukaci hukumomin tsaro da su tsaurara matakan tsaro ga zababben shugaban kasa, Bola Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Tags: