Zargin Kisan Kai: Kotu Ta Ba Da Umarnin Tilastawa AG Na Kano Gurfanar Da Doguwa
- Alhassan Doguwa, shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai na iya shiga sabuwar matsala kan zargin da ake masa na kisan kai
- Hakan ya biyo bayan wata bukata da tsohon alkalin majistare na jihar Kano ya shigar a kan tuhumar da ake yi wa Doguwa
- Umurnin ya kuma tilastawa Atoni Janar na jihar Kano da ya fara gurfanar da Doguwa
Kano - A ranar Alhamis, 27 ga watan Afrilu, wata babbar kotu da ke zama a jihar Kano, ta amince da wani kudiri da ke neman a fara tuhumar shugaban masu rinjaye a majalisar wakilai, Alhassan Doguwa kan kisan kai.
Umurnin da kotun ta bayar zai tilastawa Atoni Janar na jihar Kano fara gurfanar da Doguwa a gaban alkali, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Da farko an kama Doguwa sannan aka gurfanar da shi a gaban kotun majistare kan zargin kisan kai da kona kayayyaki a karamar hukumar Tudunwada a lokacin zaben shugaban kasa da na yan majalisar tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Daga bisani kotun ta bayar da belin shugaban masu rinjayen a majalisar bayan lauyansa ya shigar da bukatar hakan.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Sai dai kuma jim kadan bayan sakin nasa, kungiyoyin jama'a a jihar sun koka kan yadda gwamnatin jihar ta ki hukunta dan majalisar saboda kasancewarsa mamba a jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
A wani matakin gaggawa, wani tsohon alkalin jihar Kano mai ritaya, Muntari Dandago ya nemi izinin babbar kotun jihar da ta tilastawa Atoni Janar na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan gaggauta tuhumar Doguwa da sauran wadanda ake zargi da hada kai da shi.
Da take zartar da hukunci, kotun ta amince da bukatar wanda ya shigar da karar na tuhumar dan majalisar.
Har yanzu ba a kammala bincike kan lamarin Doguwa ba, Atoni Janar na Kano
A nashi martanin, Atoni Janar na jihar Kano, Musa Abdullahi Lawan, ya ce ba a kammala bincike a kan lamarin ba.
Lawan ya bayar da tabbacin cewa jihar ba za ta yi kasa a gwiwa wajen tuhumar dan majalisar ba idan bukatar hakan ya taso bayan kammala bincike kan lamarin.
Babu abun da zai hana rantsar da Tinubu, Keyamo
A wani labari na daban, karamin ministan kwadago, Festus Keyamo ya jaddada cewar babu abun da zai hana rantsar da Asiwaju Bola Tinubu, a ranar 29 ga watan Mayu sai dai wani ikon Allah.
Asali: Legit.ng