Motoci Sun Isa Sudan Don Kwashe Daliban Najeriya Da Suka Makale a Rikicin Kasar
- A yau Laraba, 26 ga watan Afrilu ne motocin da za su kwashe yan Najeriya da suka makale a Sudan ya isa wajen da suke
- Hukumar NIDCOM ta ce motocin zai kwashe daliban zuwa iyakar Masar inda daga nan za a kwashe su a jirgin sama zuwa Najeriya
- An tattaro cewa kimanin naira miliyan 150 gwamnatin tarayya ta ware domin karbo hayar motocin
Hukumar da ke kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje, NIDCOM ta ce motocin bas-bas sun isa Sudan don kwashe daliban Najeriya yayin da ake tsaka da yaki a kasar.
A cikin wata sanarwa da ta saki a ranar Laraba, hukumar NIDCOM ta ce motocin zai kwashi daliban zuwa iyakar Masar, jaridar The Cable ta rahoto.
Za a kwashi daliban a jirgi daga Habasha zuwa Najeriya
Daga nan ana sa ran za a kwashi daliban a jirgin sama daga Masar zuwa Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“A daren jiya, tawagar kwashe yan Najeriya a Sudan sun amshi wasu motocin bas-bas don kwaso daliban Najeriya zuwa iyakokin da ke kusa da Masar, kafin a kwashe su a jirgin sama zuwa Najeriya, gwamnatin tarayya ta magance wannan ta @nemanigeria da ofishin jakadancin Najeriya da ke Sudan.
“Karin motoci za su iso da safiyar nan sannan daliban da suka makale za su tashi a yau.”
Hukumar ta ce ana yi wa daliban rijista gabannin barin kasar.
Da farko mun ji cewa gwamnatin tarayya ta karbi hayar motocin bas 40 domin kwashe yan Najeriya da suka makale daga kasar da ke fama da yaki zuwa Habasha.
An tattaro cewa gwamnatin ta saki kudi naira miliyan 150 don karbo hayar motocin.
A cewar jaridar Punch, babban bankin Najeriya (CBN) ta hannun hukumar bayar da agajin gaggawa ne ya biya kudin zuwa asusun wani kamfanin sufuri a ranar Talata, 25 ga watan Afrilu, da misalin karfe 12:37 na rana.
Da yake tabbatar da hakan, Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar NidCom ta ce an biya kudin tana mai cewa za a fara kwashe su a ranar Laraba, 26 ga watan Afrilu.
Rikicin Sudan: Peter Obi ya aika muhimmin sako ga Buhari
A baya mun kawo cewa Peter Obi ya tunatar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa hakki ne da ya rataya a wuyansa ceto al'ummar kasar da suka makale a yakin Sudan.
Asali: Legit.ng