Badakalar N4.6bn, Hukumar EFCC Za Ta Sake Maka Tsohon Minista a Gaban Kotu
- Hukumar EFCC za ta sake gurfanar da tsohon ministan sufuri a gaban kotu bisa zargin wawurar dukiyar ƙasa
- EFCC na tuhumar Femi Fani-Kayode da wasu mutum uku daban bisa zargin lalata maƙudan kuɗi har N4.6bn
- Za a sake maka su Kayode gaban kotu ne bayan EFCC ta yi rashin nasara a ƙarar da ta shigar da su da farko
Jihar Legas - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa (EFCC) za ta sake tuhumar tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode da wasu mutum uku, a babbar kotun tarayya Abuja.
Channels tv ta kawo rahoto cewa za a sake gurfanar da su Fani-Kayode ne bisa zargin ɓarnatar da N4.6bn.
Lauyan hukumar EFCC, Rotimi Oyedepo (SAN), ya gaya wa alƙalin babbar kotun tarayya ta Legas, Daniel Osiagor, ranar Talata cewa, sake tuhumar Kayode ya zama tilas bayan kotun ɗaukaka ƙara a jihar Legas ta yi fatali da tuhume-tuhumen da ake mu su.
Oyedepo ya bayyana cewa duba da hukuncin kotun ɗaukaka ƙarar, dukkanin wasu hujjoji da takardun da suka gabatar, suna buƙatar a ba hukumar domin ba ta damar sake shigar da ƙara a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Premium Times ta tattaro cewa Mai shari'a Osiagor ya bayar da umurnin a miƙa wa hukumar EFCC dukkanin hujjoji da takardun da ta gabatar a lokacin sauraron ƙarar
A ranar Alhamis ta makon da ya gabata ne dai, alƙalin kotun ɗaukaka ta Legas, Mohammed Danjuma, ya yanke hukunci kan ƙarar da wacce ake tuhumar su da Fani-Kayode, tsohuwar ministan kuɗi, Nenadi Usman, inda ta ƙalubalanci hurumin babbar kotun tarayya ta Legas na sauraron ƙarar.
Mai ɗaukaka ƙarar ta kuma ce ƙarar da aka shigar a gaban kotun ta Legas akwai kura-kurai a cikin ta.
Bayanai Sun Fito Daga Tsagin Atiku, Da Yuwuwar Ba Za'a Rantsar da Tinubu a Matsayin Shugaban Ƙasa Ba
Kotun ɗaukaka ƙarar ta yanke hukunci wanda ya yi daidai da buƙatar mai shigar da ƙarar, sannan ta kuma ce babbar kotun tarayya ta Legas ba ta da hurumin sauraron ƙarar.
Kotun ta kuma ce dukkanin harkallar da ake zargin waɗanda ake ƙarar da su, sun gudanar da su ne a Abuja, saboda haka babbar kotun tarayya ta Abuja ke da hurumin sauraron ƙarar.
Wata Jam'iyya Ta Garzaya Kotu Neman a Hana Rantsar Da Tinubu
A wani rahoton na daban kuma, wata jam'iyya ta garzaya gaban kotu tana neman a hana rantsar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a matsayin sabon shugaban ƙasa.
Jam'iyyar Hope Democratic Party (HDP), na neman sai lallai an hana shugaba Buhari miƙa mulkin ƙasar nan a hannun Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng