29 Ga Watan Mayu: UK, Iran, Qatar Da Wasu Kasashe 40 Da Buhari Ya Ziyarta a Matsayin Shugaban Kasar Najeriya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin mulkinsa a matsayin jagora na daya a Najeriya cikin kasa da kwanaki 35 masu zuwa yayin da ranar 29 ga watan Maris ke kara gabatowa.
A matsayinsa na shugaban kasar Najeriya, an sha caccakar Buhari saboda kasancewarsa shugaban kasa mafi yawan tafiye-tafiye da aka taba samu a Afrika ta yamma.
A cewar jaridar The Punch, Buhari ya ziyarci kasashen duniya 40 a matsayin shugaban kasa kuma ya yi tafiye-tafiyen kasashen waje 90 a shekaru 8 a Najeriya.
Da ake nazarin shekaru 8 da ya yi a matsayin shugaban kasa, Buhari ya ziyarci akalla kasashe 43 a fadin duniya.
Kasashen da Buhari ya ziyarta sun kasance a fadin kasashen duniya kuma yawanci ziyar aiki, na ganin likita da kuma sauke farali ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng ta tattaro rukunin sunayen wadannan kasashe da ya ziyarta da kuma yadda shugaban kasar ya dungi ziyartansu yayin da yake shugabancin Najeriya.
Kasashen da Buhari ya fi ziyarta
S/N | Kasashe |
1 | Amurka |
2 | Birtaniya |
3 | Saudiyya |
4 | Habasha |
5 | Faransa |
Kasashen da Buhari ya ziyarta tsakanin sau 3-6
S/N | Kasashe |
1 | Afrika ta kudu (3x) |
2 | Hadaddiyar daular Larabawa (3x) |
3 | Ghana (3x) |
4 | Nijar (3x) |
5 | Senegal (4x) |
Kasashen da Shugaba Buhari ya ziyarta akalla sau 2
1 | Jordan |
2 | Sin |
3 | Jamus |
4 | Gambiya |
5 | Benin |
6 | Kenya |
7 | Equatorial Guinea |
8 | Côte d'Ivoire |
9 | Qatar |
10 | Chadi |
11 | Morocco |
Ga jerin sauran kasashe 22 da Buhari ya ziyarta a matsayin shugaban kasar Najeriya a kasa
1 | Belgium |
2 | Burkina Faso |
3 | Cameroon |
4 | Egypt |
5 | Guinea-Bissau |
6 | India |
7 | Iran |
8 | Japan |
9 | Liberia |
10 | Mali |
11 | Malta |
12 | Mauritania |
13 | Netherlands |
14 | Rasha |
15 | Rwanda |
16 | Poland |
17 | Portugal |
18 | Koriya ta Kudu |
19 | Spain |
20 | Sudan |
21 | Togo |
22 | Turkiyya |
Rikicin Sudan: Peter Obi ya aika muhimmin sako ga Buhari
A wani labarin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi ya bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya yi duk mai yiwuwa wajen kwashe yan Najeriya da suka makale a Sudan cewa hakki ne da ya rataya a wuyansa.
Asali: Legit.ng