Rikicin Cikin Gida: APC Ta Dakatar Da Zababben Sanata Da Dan Takarar Gwamna

Rikicin Cikin Gida: APC Ta Dakatar Da Zababben Sanata Da Dan Takarar Gwamna

  • Jam’iyyar APC a jihar Taraba ta dakatar da zababben sanatan Taraba ta kudu, Jimkuta David, kan zargin yin ayyukan da suka saba kundin tsarin mulkin jam’iyyar
  • Jam’iyyar ta kori wani dan takararta na gwamna sannan ta gargade shi kan daukar kansa a matsayin dan APC
  • Shugaban jam’iyyar a jihar, Ibrahim Elsudi, ya ce gudunmomi da kananan hukumominsu ne suka ladabtar da jiya-jigan jam’iyyar biyu sannan jihar ta tabbatar

Taraba - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen jihar Taraba ta dakatar da Jimkuta David, wani zababben sanata mai wakiltan Taraba ta kudu.

A cewar AIT, an dakatar da zababben Sanatan ne kan zargin ketare kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

APC ta dakatar da Jimkuta da wani
Rikicin Cikin Cikin Gida: APC Ta Dakatar Da Zababben Sanata Da Dan Takarar Gwamna Hoto: APC Update
Asali: UGC

Dalilin da yasa APC ta dakatar da zababben sanatanta da korar dan takararta na gwamna a Taraba

An kuma tattaro cewa jam’iyyar APC reshen jihar ta kori daya daga cikin yan takarar gwamnanta a zaben jihar, David Kente.

Kara karanta wannan

Daga karshe: INEC ta kammala zaben Adamawa, gwamna Fintiri ya koma kujerarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam’iyyar ta gargadi Kante da ya daina daukar kansa a matsayin dan APC a kowani mataki.

Korarren dan takarar ya maka dan takarar gwamnan na APC a zaben gwamna na ranar 18 ga watan Maris, Emmanuel Bwach a kotu.

Da yake magana game da matakin da aka dauka kan jiga-jigan biyu, Ibrahim Elsudi, Shugaban APC na jihar, ya ce, gudumomi da karamar hukumarsu ne suka dauki mataki a kansu.

Elsudi ya kuma bayyana cewa jam’iyyar reshen jihar ta tabbatar da hukuncin ta hanyar amincewar kwamitin zartarwar jam’iyyar na jihar.

Gwamna Ganduje ya bukaci Abba Gida-gida da ya kammala ayyukan da ya fara

A wani labarin, gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya roki Abba Kabir Yusuf, zababben gwamnan jihar da ya kammala ayyukan da gwamnatinsa ba za ta samu kammalawa ba.

Ganduje ya kuma jaddada cewar shi ya yafewa duk wanda ya yi masa laifi kuma bai riki kowa ba a ransa, inda shima ya roki jama'a da su yafe masa.

Da yake rokon a sakonsa na barka da sallah, Ganduje ya ce a yi kokari a kammala ayyukan domin amfanin al'ummar jihar da kuma ci gabansu gaba daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng