Dalibai Miliyan 1.6m Ne Za Su Zana Jarabawar JAMB a Bana 2023
- Ɗalibai masu neman shiga manyan makarantun gaba da sakandire a Najeriya sun fara zana jarabawar share fage watau UMTE 2023
- Wasu bayanai da muka tattara sun nuna cewa kusan mutane miliyan 1.6m ake sa ran zasu rubuta jarabawar bana
- Duk da ana samun tangarɗa a wurin tantance shacin yatsan masu rubuta jarabawa, JAMB ta ce zata shawo kan matsalar cikin kankanin lokaci
Hukumar shirya jarabawan shiga manyan makarantun gaba da Sakandire (JAMB) ta fara jarabawar bana UTME 2023 a faɗin Najeriya.
Bayanan da suka fito daga JAMB sun nuna cewa ɗalibai kusan miliyan 1.6m ne zasu zauna jarabawar bana a faɗin Cibiyoyin zana JAMB sama da 700.
Haka nan jadawalin ya nuna za'a kammala jarabawar ranar 12 ga watan Mayu, 2023 domin ba da damar fara jarabawar Direct Entry watau D.E.
Wakilin jaridar Punch ya ziyarci wasu daga cikin cibiyoyin zana jarabawar JAMB a Ilorin, babban birnin jihar Kwara da ke arewa ta tsakiya a Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
The Nation ta ce Yayin wannan ziyara ya gano cewa jami'an hukumar JAMB na tantance kowane ɗalibi da na'urar gane shacin yatsa gabanin shiga ɗakin rubuta jarabawar.
Sai dai wasu daga cikin masu zuwa zama jarabawar sun koka kan matsalolin da ake samu yayin tantance su, lamarin da wasu jami'an hukumar suka shaida cewa za'a warware nan ba da jimawa ba.
Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa tun da farko hukumar shirya JAMB ta tsara fara jawabawar ranar 29 ga watan Afrilu, 2023 amma daga baya ta canja tsarin.
A wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun jami'in hulɗa da jama'a na JAMB, Fabian Benjamin, ya ce an samu sauyin ranar fara jarabawar UTME ne domin samun damar kammala wasu ayyuka.
Bayanai Sun Fito Daga Tsagin Atiku, Da Yuwuwar Ba Za'a Rantsar da Tinubu a Matsayin Shugaban Ƙasa Ba
Gwamnonin arewa 2 da ke kan gaba a tseren kujerar shugaban NGF
A wani labarin kuma Zulum Da Buni Ke Kan Gaba a Tseren Zama Shugaban Kungiyar Gwamnoni NGF ta ƙasa
A al'ada ana karba-karban kujerar tsakanin kudu ada rewacin Najeriya kuma shugaban NGF na karshe da ya sauka ɗan kudu ne, gwamna Fayemi na jihar Ekiti.
Gwamna Zulum da takawaransa na jihar Benuwai sun samu goyon bayan APC da wasu gwamnoni, a halin yanzu ɗayansu ake sa ran zai karbi muƙamin.
Asali: Legit.ng