Rikicin Sudan: “Dole Ka Ceto Yan Najeriya Da Suka Makale”, Peter Obi Ga Buhari

Rikicin Sudan: “Dole Ka Ceto Yan Najeriya Da Suka Makale”, Peter Obi Ga Buhari

  • Peter Obi ya yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta gaggauta ceto yan Najeriya da suka makale a Sudan
  • Obi, dan takarar jam'iyyar Labour Party a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, ya nuna damuwarsa game da yan Najeriya 4000 da suka makale a Sudan
  • A cewar Obi duk da halin da ake ciki a kasar, hakkin ceto yan Najeriya da suka makale ya rataya ne a wuyan shugaban kasar

Peter Obi, dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ya tunatar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa babban hakki 1 da ya rataya a wuyansa shine ceto yan Najeriya da ke makale a Sudan.

An rahoto cewa kimanin yan Najeriya 4000 ne suka makale a kasar ta arewa maso gabashin Afrika sakamakon rikicin da ya barke tsakanin rundunonin soji 2. Yaki a kasar ya kasance tsakanin rundunar adawa biyu.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojoji Sun Kashe Mayaka 35, Sun Lalata Sansanonin Boko Haram a Wata Jahar Arewa

Peter Obi da Shugaba Buhari
Rikicin Sudan: “Dole Ka Ceto Yan Najeriya Da Suka Makale”, Peter Obi Ga Buhari Hoto: Femi Adesina, Peter Obi
Asali: Twitter

Bangare daya na biyayya ga shugaban hafsan soji, Abdel Fayyah al-Buthan. Daya bangaren kuma na biyayya ya Mohamed Hamdan Daglo, mataimakin Shugaban hafsan sojin kuma kwamandan rundunar RSF.

Da farko gwamnatin tarayya ta bayyana hatsarin da ke tattare da kwashe yan Najeriya da suka makale a Sudan saboda tashin hankali da ke kasar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta kuma bayyana cewa za a kwashe yan Najeriyan da suka makale nan ba da Jimawa ba bayan kafa wani kwamiti karkashin jagorancin ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama.

Hakkin Buhari ne ya ceto yan Najeriya da suka makale a Sudan, Obi

Sai dai kuma, a wasu jerin wallafa da ya yi a shafinsa na twitter, a ranar Lahadi, 23 ga watan Afrilu, Obi ya bayyana cewa yana daya daga cikin hakokin gwamnatin tarayya ta ceto yan Najeriya da suka makale.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Buhari Ya Fadi Lokacin Da Yan Najeriya Da Ke Zaune a Sudan Za Su Fara Dawowa Kasar

Yayin da yake nuna tsananin damuwa game da ci gaban, Obi ya yi kira ga gwamnatin Buhari da ta yi amfani da kowace hanya wajen ceto yan Najeriya 4000 da suka makale.

Ya ce:

“Ina bakin ciki kuka na damu da rahotannin cewa ba a kwashe yan Najeriya da suka makale a Sudan ba. Yayin da muka fahimci kalubalen da ke Sudan, muna bukatar gwamnatin tarayyar Najeriya da ta yi duk wani kokari wajen ceto kimanin yan Najeriya 4000 wadanda yawancinsu dalibai ne."

Sudan: Za a fara kwashe yan Najeriya a yau ko gobe, gwamnatin tarayya

A gefe guda, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ofishin jakadancin Najeriya a kasar Sudan na kokari don fara kwashe yan Najeriya da suka makale tsakanin yau Lahadi ko gobe Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng