Matawalle Ya Dawo Da Sarkin Da Ya Nada Gogarmar Dan Bindiga Sarauta a Zamfara
- Gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya dawo da sarkin Birnin Yandoto, Alhaji Aliyu Marafa kan kujerarsa
- Matawalle ya dai dakatar da basaraken ne bayan ya baiwa gogarmar dan bindiga, Ado Aleiru sarauta
- Kwamitin binciken lamarin da ke tattare nadin ne suka bayar da shawarar mayar da shi kujerarsa bayan rashin hujja ko gano alaka tsakanin sarkin da yan bindiga
Zamfara - Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara ya mayarwa Alhaji Aliyu Garba Marafa rawaninsa a matsayin sarkin Birnin Yandoto, Daily Trust ta rahoto.
A watan Yulin bara ne Matawalle ya dakatar da basaraken saboda ya baiwa gogarmar dan bindiga, Ado Aleiru sarauta.
Ana tsaka da takaddama kan nadin nasa, sai basaraken ya ce an karrama Alieru ne saboda rawar ganin da ya taka yayin kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin masarautar da yan bindigar da suka addabi karamar hukumar Tsafe.
A wata sanarwa da ya saki a ranar Lahadi, 23 ga watan Afrilu, Kabiru Balarabe Sardauna, sakataren gwamnatin jihar ya sanar da mayar da sarkin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sardauna ya ce an dawo da Marafa ne bisa la'akari da shawarwarin da kwamitin da aka kafa don gudanar da bincike kan lamarin ya bayar cewa "Kwamitin bai samu wani hujja na mugun nufi ko hadaka tsakanin sarkin da yan bindigar ba."
Ana sanya ran basaraken zai koma kujerarsa nan take, rahoton TVC News.
Sanarwar ta ce:
"Wannan domin sanar da jama'a cewa mai girma gwamnan jihar Zamfara, Hon. Bello Mohammed Matawalle, MON, (Shatiman Sokoto), ya amince da mayar da Alhaji Aliyu Garba Marafa a matsayin sarkin Birnin Yandoto.
"An dawo da shi ne saboda shawarwarin da kwamitin da aka kafa don bincike lamuran da ke tattare da sarautar da aka baiwa tubabben dan bindiga, Ado Aleiru. Kwamitin bai samu wani hujja ko mugun nufi tattare da nadin ko hadaka tsakanin sarkin da yan bindiga.
Dan Allah a Kawo Mana Agaji, Kasashe Na Ta Kwashe Mutanensu Ban Da Mu", Dalibar Najeriya Da Ta Makale a Sudan Ta Koka
"Bisa ga binciken kwamitin, an baiwa tubabben dan bindigan sarautar ne daga kokarin da ake na kulla zaman lafiya tsakanin tubabben dan bindigan da garuruwan da ke fama da ta'addanci a kananan hukumomin Tsafe da Gusau, wanda suka hada da garin Yandoto. Mayarwar nasa zai fara aiki nan take"
Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram 35 a jihar Borno
A wani labarin, dakarun sojojin Najeriya sun yi nasarar halaka mayakan kungiyar ta'addanci na Boko Haram 35 a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.
Asali: Legit.ng