Yakin Sudan: Buhari Zai Fara Kwashe Yan Najeriya Zuwa Wurin Da Akwai Zaman Lafiya a Yau Ko Gobe

Yakin Sudan: Buhari Zai Fara Kwashe Yan Najeriya Zuwa Wurin Da Akwai Zaman Lafiya a Yau Ko Gobe

  • Garba Shehu, kakakin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na kokari wajen kwashe yan Najeriya da suka makale a Sudan
  • Shehu ya jaddada cewar ofishin jakadancin Najeriya a kasar na aiki tare da gwamnatocin Sudan da Habasha don tabbatar da tsaron yan Najeriya da abun ya shafa
  • A cewarsa, ana sanya ran za a kwashe yan Najeriyan da suka makale zuwa wani waje mai zaman lafiya tsakanin yau da gobe

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a kwashe yan Najeriya da ke makale a yakin kasar Sudan zuwa wani wuri da ke da zaman lafiya a yau Lahadi, 23 ga watan Afrilu da Litinin, 24 ga watan Afrilu.

Garba Shehu, babban mai ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin labarai shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya saki a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Dan Allah a Kawo Mana Agaji, Kasashe Na Ta Kwashe Mutanensu Ban Da Mu", Dalibar Najeriya Da Ta Makale a Sudan Ta Koka

Shugaban kasa Muhammadu Buhari
Yakin Sudan: Buhari Zai Fara Kwashe Yan Najeriya Zuwa Wurin Da Akwai Zaman Lafiya a Yau Ko Gobe Hoto: MBuhari
Asali: Twitter

Yaushe za a kwashe yan Najeriya da suka makale a Sudan?

Ku tuna cewa yan Najeriya na ta matsawa gwamnatin tarayya kan ta gaggauta kwaso yan kasar musamman dalibai daga kasar da ke fama da yaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kasar Sudan ta tsinci kanta a cikin sabon yaki yayin da shugabannin soji biyu ke fada a kan mulkin kasar.

A yan awanni da suka gabata, rundunar sojin kasar sun ta baiwa kasashen waje damar kwashe jakadu da yan kasarsu, kuma tuni wasu kasashen suka fara yin hakan, ciki harda kasar Amurka.

Garba Shehu ya fadi halin da ake ciki game da yan Najeriya da ke Sudan

Da yake martani a kan ci gaban, Shehu ya ce gwamnatin tarayya na iya bakin kokarinta don tabbatar da ganin cewa an kwashe dalibai da sauran yan Najeriya da ke cikin tashin hankali a kasar zuwa wani waje mai zaman lafiya tsakanin yau da gobe.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun makale, Saudiyya da wasu kasashen sun fara debe 'ya'yansu a Sudan

Ya bayyana cewa ofishin jakadancin Najeriya a Khartoum na aiki tare da gwamnatocin Sudan da Habasha kuma cewa ministan harkokin waje na Najeriya, Geoffry Onyema, shine shugaban kwamitin da ke da alhakin kwashe yan Najeriya da suka makale.

Ya ce:

"Gwamnatin Najeriya bata iya bacci biyo bayan rikicin Sudan. Jami'anmu na aiki sosai, sun hada kai da ofishin jakadanci a Khartoum, gwamnatocin Sudan da Habasha suna kokarin tabbatar da tsaron yan kasarmu a chan."

Ga wallafar tasa a kasa:

Dalibar Najeriya a Sudan ta koka, ta ce suna cikin wani hali

A gefe guda, mun ji a baya cewa daya daga cikin daliban Najeriya da ke makale a kasar Sudan ta nemi gwamnati ta zo ta kwashe su domin suna cikin wani irin yanayi na tashin hankali.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng