Muna Kewaye Da Miyagu, Dalibar Najeriya Da Ta Makale a Sudan Ta Roki Gwamnati Ta Zo Ta Kwashe Su

Muna Kewaye Da Miyagu, Dalibar Najeriya Da Ta Makale a Sudan Ta Roki Gwamnati Ta Zo Ta Kwashe Su

  • Har yanzu daliban Najeriya da ke karatu a Sudan suna nan makale a kasar yayin da ake ci gaba da yaki
  • Wata dalibar Najeriya da ta yi nasarar isa bodar Sudan da Habasha ta koka ta ce suna cikin mawuyacin hali
  • Ta ce yawancin kasashe da suka hada da Malawi, Siriya, Ghana da sauransu sun turo a kwashe yan kasarsu

Wata dalibar Najeriya da ta makale a Sudan ta ce ita da sauran dalibai da suka makale a yakin kasar suna kewaye da masu laifi, Daily Trust ta rahoto.

Kimanin yan Najeriya 4000 ne suka makale sakamakon yakin da ake tsakanin rundunar da ke biyayya da shugaban hafsan sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, da na mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo, wanda ke jagorantar RSF.

An kashe daruruwan mutane tun bayan da yakin ya barke tsakanin rundunonin janar-janar din biyu a Khartoum, babban birnin kasar Sudan.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun makale, Saudiyya da wasu kasashen sun fara debe 'ya'yansu a Sudan

Birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan
Muna Kewaye Da Miyagu, Dalibar Najeriya Da Ta Makale a Sudan Ta Roki Gwamnati Ta Zo Ta Kwashe Su Hoto: ABC News
Asali: UGC

Fauziyya Idris Safiyo, wata dalibar Najeriya da ta yi nasarar tserewa daga Khartoum zuwa garin da ke kan iyakar Sudan da Habasha, ta ce lamarin na kara tabarbarewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta ce:

"Muna iya jiyo karar harbi da fashe-fashen bam daga kowani bangare. jiragen yaki ma na ta luguden wuta. Babu abinci, ruwa da magani. Ba mu iya zuwa koina ba. Ba mu da isasshen kudi kuma akwai masu aikata laifi ta kowaina."

A cewarta, kasashe da dama sun fara kwashe yan kasarsu sai dai kuma babu wani abu dangane da kwashe yan Najeriya a kasar da ke yankin gabashin Afrika.

Ta kara da cewar:

"Yan Najeriya ne kawai aka bari makale ga mata da yawa a cikinmu, kasashe kamar su Habasha sun ki barin yan Najeriya su shiga kasarsu ba tare da biza ba."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Wani gini ya ruguje a barikin 'yan sanda, ya kashe, ya danne mutane da yawa

"Yawancin daliban na cikin tashin hankali inda wasu abincinsu ya kare za ka ga yan kasar ma suna guduwa."

Da yake magana game da halin da ake ciki, Muhammad Nura Bello, shugaban daliban Najeriya a jami'ar kasa da kasa ta Sudan ya ce babu wuta ko ina ya yi duhu hatta su ma yan Sudan din barin kasar suke yi.

Ba zai yiwu a kwashe daliban Najeriya da ke makale a Sudan ba a yanzu, Gwamnatin tarayya

A halin da ake ciki, gwamnatin Najeriya na kokarin kwashe daliban Najeriya a Suda sai dai ta ce aikatan hakan na da matukar hatsari a yanzu haka saboda haka ba mai yiwuwa bane.

Abike Dabiri-Erewa, shugabar hukumar kula da yan Najeriya mazauna waje ta bayyana cewa hukumomi sun kammala duk wasu tsare-tsare na kwashe daliban amma hakan ba zai yiwuwa ba saboda halin da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng