Musulmai Sun Yaba Wa Yan Kabilar Ibo da Suka Gudanar da Karamar Sallah a Enugu
- Wasu Musulmai 'yan kabilar Igbo sun ja hankalin mutane da yawa a soshiyal midiya ganin yadda suka yi ƙaramar Sallah
- Da yawan Musulmai a Tuwita sun nuna mamakinsu da ganin Musulunci ya shiga har cikin inyamurai a Najeriya
- A ranar Jumu'a 21 ga watan Afrilu, Musulman Najeriya suka gudanar da Eid-el-Fitr bayan ganin jinjirin watan Shawwal
Enugu - Mabiya addinin Musulunci 'yan kabilar Ibo da suka yi Sallah ƙarama a jihar Enugu sun sha yabo daga yan uwansu a shafin sada zumunta Tuwita.
Hakan ta faru ne bayan bidiyo ya watsu a Tuwita, inda aka ga wani mutumi, Siraj Nwansukka, ya jagorancin sauran jama'a kuma ya yi huɗuba a harshen Ibo ranar Jummu'a.
Punch ta ce an ɗauki bidiyon Nwansukka ranar 21 ga watan Afrilu, 2023 daidai da 1 ga watan Shawwal, 1444AH a filin idi na garin Alor-Agu, wanda Musulmai suka fi rinjaye, ƙaramar hukumar Eze ta kudu, jihar Enugu.
Zuwa yanzu akalla mutane 2000 suke tura bidiyon ga abokanansu, sama da 200 suka tofa albarkacin bakinsi yayin da fiye da 5,000 suka kalli bidiyon.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Martanin mutane a soshiyal midiya
Mudashiru Temitope ya ce:
"Karo na farko kenan da na ga Ibo musulmai, gunin sha'awa, Masha Allah, muna fatan Allah ya karbi ibadunmu."
Wata Amaka Ogili ta rubuta cewa:
"Kawuna ya mutu a cikin addinin Musulunci, duk ɗaya muke bamu nuna wa juna wariya."
Yayin da yake nuna mamakin da ya shiga bayan ganin bidiyon, Daddy Evra ya ce:
"Wai dagaske? Na kasa yarda da abinda nake gani, ko kunsan ina yawan tunani a kan haka? A takaice dai akwai Ibo musulmai? Allahu Akbar."
A wani martanin kuma, Phanini ya ce, "Karo na farko kenan da naga Musulmai yan ƙabilar Ibo."
Wani mai suna Abdul-Afeez ya kara da cewa:
"Maganar gaskiya wannan sabon abu ne a wurina amma fa duk da haka ban yi mamaki ba saboda abinda Allah ya faɗa a cikin littafinsa mai tsarki Alƙur'ani."
Wani Mutumi Ya Daɓa Wa Lamami Wuka
A.wani labarin kuma Mutumi Ya Daɓa Wa Lamami Wuka Ana Tsaka da Sallar Asuba a Cikin Watan Azumi
An tattaro cewa mutumin ya kutsa kai lokacin da aka tafi Sujjada, ya shiga har wurin liman ya caka masa wuƙa sau biyu.
Asali: Legit.ng